'Yan kungiyar Boko haram sun shiga matsala: Wani hakimi ya tona musu asiri

'Yan kungiyar Boko haram sun shiga matsala: Wani hakimi ya tona musu asiri

Hakimin garin Duhu na jihar Adamawa, Mohammed Sanusi ya ce bisa ga dukkan alamu 'yan ta'addan da suka kai hari a garin Michika da ke makwabtaka da su a daren Litinin suna neman abinci da kudi da magunguna ne.

Mazauna garin sun ce 'yan ta'addan sun kai farmaki ne ta Kofar Borno da Kofar Adamawa inda suka rika harbe-harbe wanda hakan yasa mutane suka tsere cikin daji.

Da yawa cikin mazauna garin sun shaidawa Punch cewa sunyi kwanan daji ne a ranar yayin da aka kashe mutane bakwai duk da cewa 'yan sanda sun ce farar hula biyar aka kashe kuma 'yan ta'adda 11 sun mutu a harin.

DUBA WANNAN: Rarara ya yi karin haske a kan rahotannin kai masa hari

'Yan kungiyar Boko haram sun shiga matsali, wani hakimi ya tona musu asiri
'Yan kungiyar Boko haram sun shiga matsali, wani hakimi ya tona musu asiri
Asali: UGC

A hirar da ya yi da majiyar Legit.ng a ranar Laraba, Hakimin garin, Sanusi ya ce 'yan ta'addan sunyi fashi a gidajen man fetur, shagunan magani da kayan masarufi, sun kuma bar manyan motocci uku makil da kayan abinci da suka sato bayan sojoji sun fatattake su.

Ya ce, "Yan ta'addan sun shigo ta hanyar da suka saba zuwa da motocci masu yawa. Sun cika motoccin da man fetur da kayayakin abinci daga shaguna. Sun kuma yi kutse a shagunan magani inda suka neman magungunan da za su bawa mambobinsu.

"Sun kuma kai hari Union Bank da ke garin inda su kayi amfani da nakiya suka fasa dakin ajiyar kudi amma mun ji wai ba su samu kudi ba saboda an cewa wata motar daukan kudi ta tafi da kudaden zuwa Central Bank da ke Yola."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel