Jam'iyyar PDP tayi barazanar kauracewa zaben ranar Asabar a Bauchi

Jam'iyyar PDP tayi barazanar kauracewa zaben ranar Asabar a Bauchi

Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP reshen jihar Bauchi tayi ikirarin cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ba za tayi adalci ba a lokacin da za a cigaba da kidaya kuri'un karamar hukumar Tafawa Balewa da ake dage a ranar 9 ga watan Maris a jihar.

Idan ba a manta ba a ranar Talata ne wata Babban Kotun Tarayya ta umurci INEC ta dakatar da cigaba da kidaya kuri'un karamar hukumar Tafawa Balewa.

Sai dai a wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar a ranar Alhamis, Shugaban jam'iyyar na jihar, Hamza Akuyam ya yi rantsuwa cewa za a gudanar da zaben raba gardama ba a jihar har sai an kammala kidaya kuri'un karamar hukumara Tafawa Balewa kuma an bayyana sakamakon.

DUBA WANNAN: Kano: Na hannun daman Atiku ya kare shi a kan goyon bayan Abba Gida-Gida

Jam'iyyar PDP tayi barazanar kauracewa zaben ranar Asabar a Bauchi
Jam'iyyar PDP tayi barazanar kauracewa zaben ranar Asabar a Bauchi
Asali: Twitter

"Amincewa da zaben rabar gardama ba tare da kidaya kuri'un zaben farko ba daidai ya ke da sake rubuta jarabawa ba tare da ganin sakamakon jarabawar na farko ba," inji shi.

Shugaban jam'iyyar ya yi ikirarin cewa da gangan baturen zabe na jihar ya rika jinkirin kidaya kuri'un har zauwa karfe 2 na rana inda ya fito da takardan kotu na cewa a dakatar da kidayan sakamakon zaben.

Sanarwar ta cigaba da cewa: "Jam'iyyar PDP reshen jihar Bauchi ta lura cewa sanarwar da baturen zabe na jihar Bauchi, Alhaji Ibrahim Abdullahi ya yi na cewar zai yi zaben raba gardama da janyo hankulan mutane da yawa a wajen jihar.

"Hakan yasa jam'iyyar PDP ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki kuma ta ga ya dace da sanar da al'umma matsayan ta.

"Idan ba a manta ba kwamitin da INEC ta kafa domin a kan zaben ranar 9 ga watan Maris a jihar Bauchi sun tabbatar da sahihancin zaben da kuri'un da al'ummar Bauchi suka kada.

"Hedkwatan na INEC ta bayyana cewa babu bukatan a sake zaben raba gardama kuma ta bayar da umurnin a kammala kirga kuri'un karamar hukumar Tafawa Balewa a ranar 19 ga watan Maris na 2019.

"Dukkan jam'iyyu sun amince da wannan matakin amma banda APC.

"Hakan yasa mu kayi mamaki da baturen zabe na jihar Bauchi ya ce zai sake gudanar da zabukan raba gardama a ranar 23 ga watan Maris na 2019 a wasu kananan hukumomi a Jihar.

"Wannan ne yasa muka bukatar da dage gudanar da zaben raba gardamar da aka shirya yi a ranar 23 ga watan Maris a wasu mazabu har sai an kammala kidiya kuri'un karamar hukumar Tafawa Balewa an hada da na sauran kananan hukumomi 19 da aka kidiya domin samun sakamako na gaskiya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel