Yanzu Yanzu: Hukumar INEC ta sanya ranar 13 ga watan Afrilu don sake zabe a Rivers

Yanzu Yanzu: Hukumar INEC ta sanya ranar 13 ga watan Afrilu don sake zabe a Rivers

- Hukumar zabe mai zaman kanta ta shirya sake zaben jihar Rivers a ranar Asabar, 13 ga watan Afrilu

- Festus Okoye, kwamishinan bayanai da wayar da kan masu zabe na hukumar INEC, ne ya sanar da hakan

- Okoye yace za a sanar da sakamakon zaben a ranar 15 ga watan Afrilu yayinda bayar da takardar shaidar cin zabe zai kasance a ranar 19 ga watan Afrilu

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta shirya sake gudanar da zabe a jihar Rivers a ranar Asabar, 13 ga watan Afrilu.

Festus Okoye, kwamishinan bayanai da wayar da kan masu zabe na hukumar INEC, ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 21 ga watan Maris.

Yanzu Yanzu: Hukumar INEC ta sanya ranar 12 ga watan Afrilu don sake zabe a Rivers
Yanzu Yanzu: Hukumar INEC ta sanya ranar 12 ga watan Afrilu don sake zabe a Rivers
Asali: Original

Okoye ya kara da cewar sanar da sakamakon zaben zai kasance a ranar 15 ga watan Afrilu yayinda bayar da takardar shaidar cin zabe zai kasance a ranar 19 ga watan Afrilu.

A bangare guda, Legit.ng ta rahoto cewa ba za a gudanar da zaben kece raini da aka shirya yi a ranar Asabar a jihar Adamawa ba.

KU KARANTA KUMA: Ganduje yayi wuta inda ya kaddamar da karin ayyuka a Gama yan kwanaki kafin zabe (hotuna)

Wannan ya biyo bayan karar da dan takarar gwamna na jam'iyyar Movement For Restoration and Defense for Democracy (MRDD), Mustapha Shaba ya shigar a kotu na dakatar da INEC daga gudanar da zaben.

Shaba ya shigar da karar ne saboda INEC ba ta sanya tambarin jam'iyyarsa ba takardun kada kuri'a da akayi amfani da su a zaben ranar 9 ga watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel