Ta tabbata: Ba za ayi zaben gwamna a Adamawa ba, kotu ta yanke hukunci

Ta tabbata: Ba za ayi zaben gwamna a Adamawa ba, kotu ta yanke hukunci

Rahoton da muka samu daga The Cable na nuni da cewa ba za a gudanar da zaben kece raini da aka shirya yi a ranar Asabar a jihar Adamawa ba.

Wannan ya biyo bayan karar da dan takarar gwamna na jam'iyyar Movement For Restoration and Defense for Democracy (MRDD), Mustapha Shaba ya shigar a kotu na dakatar da INEC daga gudanar da zaben.

Shaba ya shigar da karar ne saboda INEC ba ta sanya tambarin jam'iyyarsa ba takardun kada kuri'a da akayi amfani da su a zaben ranar 9 ga watan Maris.

Ta tabbata: Ba za ayi zaben gwamna a Adamawa ba, kotu ta yanke hukunci
Ta tabbata: Ba za ayi zaben gwamna a Adamawa ba, kotu ta yanke hukunci
Asali: UGC

Da farko dai kotun ta bawa INEC damar tayi zaben kece rainin amma daga bisani sai ta ce a dakatar da zaben sakamakon umurin da kotu ta bayar na yin hakan.

DUBA WANNAN: Kano: Na hannun daman Atiku ya kare shi a kan goyon bayan Abba Gida-Gida

A baya, Kwamishina zabe na jihar Adamawa, Kassiam Gaidam ya ce dokar zabe ba ta bawa kotu ikon dakatar da zaben ba kuma bai san da maganar dakatar da zaben ba.

Sai kuma daga baya a ranar Laraba, Gaidam ya bayyana cewa kotu ta bayar da umurnin dakatar da gudanar da zaben kece rainin.

Ya kara da cewa ba kotu ne za ta yanke hukunci a kan yiwuwar zaben ko akasin haka ba.

"Ina son in tabbatar muku da cewa kotu ta aike da hukunci zuwa hedkwatan mu na INEC kuma kama yadda al'adarmu ta ke na yiwa kotu biyaya, za muyi biyaya ga umurnin amma zamu kallubalanci hukuncin a kotu," inji shi.

"Za mu saurari hukuncin da kotu za ta yanke a kan karar da muka shigar zuwa gobe."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel