Rundunan yan sandan Edo ta ceto basaraken da masu garkuwa da mutane suka sace

Rundunan yan sandan Edo ta ceto basaraken da masu garkuwa da mutane suka sace

- Yan sanda sun ceto sarkin garin Ukhiri da ke karamar hukumar Ikpoba-Okha na jihar Edo wanda masu garkuwa da mutane suka sace shi

- Sashin masu yaki da masu garkuwa da mutane na rundunar yan sandan Edo ne suka ceto basaraken

- Rundunar yan sandan ta bayyana cewa ba a biya kundin fansa ba a kan shi

Rundunan yan sandan Najeriya reshen jihar Edo, ta tabbatar da ceto Enogie Godwin Aigbe, basaraken garin Ukhiri, a karamar hukumar Ikpoba-Okha dake jihar.

DSP Chidi Nwabuzor, kakakin rundunar ne ya tabbatar da lamarin ga Kamfani Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Benin a ranar Alhamis, 21 ga watan Maris.

Rundunan yan sandan Edo ta ceto basaraken da masu garkuwa da mutane suka sace
Rundunan yan sandan Edo ta ceto basaraken da masu garkuwa da mutane suka sace
Asali: Depositphotos

Nwabuzor ya bayyana cewa jami’ai daga sashin masu hana garkuwa da mutane ne suka ceto basaraken, karkashin jagorancin SP Balogun Richard, wanda ya dauki matakin bayan samun rahoton kwararru.

Yace an ceto basaraken ne a deren Laraba, 20 ga watan Maris da misalin karfe 10:00 na dare a yankin Sakponba dake yankin.

Yan bindiga sun yi garkuwa da Aigbe ne ranar Asabar, 16 ga watan Maris a fadarsa.

KU KARANTA KUMA: Ganduje yayi wuta inda ya kaddamar da karin ayyuka a Gama yan kwanaki kafin zabe (hotuna)

Masu garkuwan sunyi nasarar tattaunawa da iyalensa inda suka bukaci a biya kudin fansa a kudaden kasar waje.

Sai dai, Nwabuzor ya bayyana cewa ba a biya kudin fansan ba kafin ceto shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel