Ganduje yayi wuta inda ya kaddamar da karin ayyuka a Gama yan kwanaki kafin zabe (hotuna)

Ganduje yayi wuta inda ya kaddamar da karin ayyuka a Gama yan kwanaki kafin zabe (hotuna)

Gwamnatin jihar ta rarraba jakunkunan haihuwa sama da 10,000 ga mata masu ciki a jihar wanda farashinsu ya kai kimanin naira miliyan 150.

An gudanar da shirin rabon ne a kananan hukumomi 15 inda kowace jaka ke dauke da abunda mata masu ciki ke bukata a lokacin haihuwa.

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan a ranar Laraba, 20 ga watan Maris lokacin da yake kaddamar da shirin rabon kayayyakin mata 2000 wanda aka gudanar a cibiyar lafiya ta Gama, katamar hukumar Nasarawa da ke jihar.

Ganduje ya samu walkilcin mataimakinsa, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna wanda ya bayyana cewa gwamnati mai ci ta mayar da hankali sosai wajen kula da mata masu ciki kyauta a jihar.

Ganduje yayi wuta inda ya kaddamar da karin ayyuka a Gama yan kwanaki kafin zabe (hotuna)
Mataimakin gwamnan jihar Kano, Gawuna yayinda yake rabon jakunkunan haihuwar ga mata
Asali: Facebook

Gwamna Ganduje ya bayyana cewa gwamnatinsa ta shirya wani horo na watanni 18 kan karban haihuwa wanda bayan horarwar za ta tura ma’aikatan zuwa yankin karkara domin karbar haihuwa cikin sauki.

Ganduje yayi wuta inda ya kaddamar da karin ayyuka a Gama yan kwanaki kafin zabe (hotuna)
Ganduje yayi wuta inda ya kaddamar da karin ayyuka a Gama yan kwanaki kafin zabe
Asali: Facebook

A cewar gwamnan, kimanin unguwar zoma 1,936 aka baiwa horo na musamman kan yadda za a magance kalubale akan aikin, inda ya kara da cewa jihar ta kuma samar da adaidaita sahu da zai dunga daukar masu ciki zuwa asibitoci.

KU KARANTA KUMA: Namijin kishi: Miji ya kashe kwarton matarshi

Ganduje yayi wuta inda ya kaddamar da karin ayyuka a Gama yan kwanaki kafin zabe (hotuna)
Ganduje yayi wuta inda ya kaddamar da karin ayyuka a Gama yan kwanaki kafin zabe
Asali: Facebook

Ya kuma bayyana cewa kwanan nan aka kamala shirin duba idanu kyauta a asibitin Isa Kaita inda mutane sama da 150 suka amfana, sannan kuma cewa an yi gagarumin nasara a aiki, sannan ya kuma bayyana cewa sama da mutane 3000 da ke fama da matsalar ido sun samu magani da madubin idanu.

Daga karshe gwamnan ya ba mutane tabbacin cewa gwamnati mai mulki ta jajirce wajen kaddamar da Karin ayyuka domin inganta rayuwarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel