Da dumin sa: Farashin Naira ya fadi warwas a kasuwannin hada-hadar kudade

Da dumin sa: Farashin Naira ya fadi warwas a kasuwannin hada-hadar kudade

Farashin kudin Naira na Najeriya mun samu labarin cewa ya fadi kasa war was a kasuwannin hada-hadar kudade na bayan fage a manyan birane irin su Legas a ranar Laraba inda aka rika sayar da dalar Amurka akan Naira 358.2 sabanin Naira 358 da aka sayar da ita ranar Talata.

Haka zalika kamar yadda majiyar mu ta kamfanin dillacin Labaru ta ruwaito mana, ana siyar da kudin kasar Birtaniya na Fan akan Naira 472 yayin da kuma kudin tarayyar turai na Euro ake siyar da shi akan Naira 408.

Da dumin sa: Farashin Naira ya fadi warwas a kasuwannin hada-hadar kudade
Da dumin sa: Farashin Naira ya fadi warwas a kasuwannin hada-hadar kudade
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Abun da yasa muka garzaya kotu kan zaben Buhari - Obi

A wani labarin kuma, Mista Godwin Emefiele, shugaban babban bankin Najeriya watau Central Bank of Nigeria (CBN) ya bayyana cewa 'yan Najeriya na kashe kudaden da suka kai akalla Dalar Amurka miliyan dari biyar a duk shekara wajen shigo da man ja daga kasashen waje.

Shugaban Central Bank of Nigeria (CBN) din yayi wannan ikirarin ranar Litinin din da ta gabata da yake jawabi a wajen wani taron masu ruwa da tsaki na masu sana'ar man ja a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Taron dai kamar yadda muka samu ya samu halartar gwamnonin jahohin Akwa Ibom, Edo da Abiya. Haka ma shugabanni daga kamfanonin 'yan kasuwa kamar su Dangote, Flour Mills, United Food Industries da ma Dufil Prima Foods Plc dukkan su sun halarci taron.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel