Hanyoyin da za bi don kawo karshen yan bindiga a Zamfara – Gwamna Yari

Hanyoyin da za bi don kawo karshen yan bindiga a Zamfara – Gwamna Yari

- Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya bayyana hanyar da ya kamata a bi wajen shawo kan matsalar yan ta'adda a jihar

- Yari yace sai sun hada kai da gwamnatocin da ke makwabtaka da su sannan za a cimma nasarar yin haka

- Gwamnan ya kuma jadadda cewar akwai bukatar a bai wa sojoji manyan bindigogi wajen yaki da yan ta’addan da ke yankin

Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ya bayyana cewa har sai gwamnatocin jihohin da ke makwabtaka da su sun hada kai, kafin a samo bakin zaren fatattakar yan ta’addan da suka buwayi yankin.

Yari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake hira da shafin BBC a ranar Laraba, 20 ga watan Maris.

Wasu yankunanarewa musamman jihar Zamfara dai na fama da matsaloli da hare-haren yan bindiga kama daga masu fashin shanu zuwa masu garkuwa da mutane.

Gwamnan ya jadadda cewar akwai bukatar a bai wa sojoji manyan bindigogi wajen yaki da yan ta’addan da ke yankin.

Hanyoyin da za bi don kawo karshen yan bindiga a Zamfara – Gwamna Yari
Hanyoyin da za bi don kawo karshen yan bindiga a Zamfara – Gwamna Yari
Asali: UGC

Hakazalika Yari ya ce karfin maharan "bai yi kusa da na dakarun tsaron Najeriya ba."

Ya ce maharan suna amfani ne da bindigogi "na al'ada" wato kanannan bindigogi.

A karshe ya ce ya kamata sojoji su nuna wa wadannan maharan ba sani, ba sabo wajen yaki da su.

KU KARANTA KUMA: Namijin kishi: Miji ya kashe kwarton matarshi

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa kimanin rayukan mutane 10 sun salwanta a wani sabon hari da ake zargin makiyaya da ya auku cikin kauyen Tse loreleegeb da ke karkashin karamar hukumar Guma a jihar Benuwe.

Shafin jaridar Vanguard ya ruwaito cewa, hukumar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da salwantar rayukan mutane biyar yayin aukuwar wannan mummuman hari cikin duhu a dare.

Rahotanni sun bayyana cewa, maharan da suka kutso daga makociyar jiha ta Nasawara a daren Talata sun yi aman wuta na harsashin bindiga kan duk wanda suka riska.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel