INEC ta fidda sunayen jihohi 18 da za ta gudanar da zaben cike gurbi a ranar Asabar

INEC ta fidda sunayen jihohi 18 da za ta gudanar da zaben cike gurbi a ranar Asabar

- Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta fidda sunayen jihohi 18 da za ta gudanar da zaben cike gurbi a ranar Asabar

- INEC ta ce karashen zaben gwamna zai gudana cikin jihohi biyar na Najeriya

- Hukumar INEC ta wassafa adadin kananan hukumomi da karashen zaben zai gudana cikin jihohi 18 na Najeriya

A ranar Alhamis, 21 ga watan Maris, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC, ta fidda sunayen jihohi 18 da zaben cike gurbi da kuma karashen zabe zai gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

INEC ta fidda sunayen jihohi 18 da za ta gudanar da zaben cike gurbi a ranar Asabar
INEC ta fidda sunayen jihohi 18 da za ta gudanar da zaben cike gurbi a ranar Asabar
Asali: UGC

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, rahoton da hukumar INEC ta fitar ya bayyana yadda zaben cike gurbi na gwamna zai gudana cikin wasu jihohi 5 da Najeriya ta kunsa.

1. Bauchi (Karamar Hukuma daya)

2. Bayelsa (Kananan Hukumomi uku)

3. Benue (Kananan Hukumomi tara)

4. Ebonyi (Kananan Hukumomi uku)

5. Edo (Karamar Hukuma daya)

6. Ekiti (Karamar Hukuma daya)

7. Kaduna (Karamar Hukuma daya)

8. Adamawa (Kananan Hukumomi biyu)

9. Kano (Karamar Hukuma daya)

10. Kogi (Kananan Hukumomi uku)

11. Imo (Kananan Hukumomi biyar)

12. Lagos (Karamar Hukuma daya))

13. Nasarawa (Kananan Hukumomi hudu)

KARANTA KUMA: Kotu ta bai wa Shehu Sani damar bincikar kayan zabe na INEC

14. Osun (Karamar Hukuma daya)

15. Plateau (Karamar Hukuma daya)

16. Sokoto (Kananan Hukumomi biyu)

17. Taraba (Kananan Hukumomi biyu)

18. Abuja (Kananan Hukumomi hudu)

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel