Kotu ta bai wa Shehu Sani damar bincikar kayan zabe na INEC

Kotu ta bai wa Shehu Sani damar bincikar kayan zabe na INEC

Sanata mai wakilcin shiyyar Kaduna ta Tsakiya a zauren majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani, ya samu lasisin gudanar da bincike kan kayayyakin zabe da hukumar INEC ta ribata yayin babban zaben kasa na ranar 23 ga watan Fabrairun 2019.

Kotu ta bai wa Shehu Sani damar bincikar kayan zabe na INEC
Kotu ta bai wa Shehu Sani damar bincikar kayan zabe na INEC
Asali: Twitter

Bisa ga amincewar kotun daukaka da sanadin hukuncin mai shari'a A.H Suleiman, Sanata Sanata yayin fafutikar sa ta kalubalantar sakamakon zaben Sanatan shiyyar Kaduna ta Tsakiya zai gudanar da bincike kan kayayyakin zabe da hukumar INEC ta ribata.

Umarnin kotun ya biyo bayan korafi mai lamba EPT/KD/SN/M/02/19 da Sanata Shehu Sani na jam'iyyar PRP ya shigar a yayin yunkurin sa na ci gaba da kalubalantar sakamakon zaben da ya gudana makonni kadan da suka gabata.

Cikin korafin da Sanatan shigar, ya nemi Kotu ta tursasawa INEC ba shi damar gudanar da bincike kan wasu muhimman kayayyakin da ribata yayin zaben da suka hadar da takardun sakamakon zabe.

KARANTA KUMA: Zaben cike gurbi a jihar Bauchi da Adamawa na nan daram kamar yadda muka tanada - INEC

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Shehu Sani na kalubalantar sakamakon zaben hukumar da ta kaddamar da dan takara na jam'iyyar APC, Uba Sani, a matsayin wanda ya yi nasara yayin zaben kujerar sanatan shiyyar Kaduna ta Tsakiya.

Kazalika dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu, Atiku Abubakar, na ci gaba da kalubalantar sakamakon zaben wanda a halin yanzu ya gabatar da wasu dalilai da korafe-korafe biyar a gaban Kuliya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel