Garkuwa da Mutane, Satar Shanu, rikicin Makiyaya da Manoma sun fi ta'addancin Boko Haram muni - Dan Ali

Garkuwa da Mutane, Satar Shanu, rikicin Makiyaya da Manoma sun fi ta'addancin Boko Haram muni - Dan Ali

Da yawa da cikin manyan kalubale da kuma barazana ta rashin tsaro da ke addabar kasar nan musamman rikicin makiyaya da manoma, garkuwa da mutane, da kuma satar shanu sun yiwa ta'addanci Boko Haram ta fuskar muni kamar yadda Ministan tsaro, Mansur Dan Ali ya bayyana.

Ministan tsaro na Najeriya Mansur Muhammad Dan Ali, ya bayyana cewa, ta'addancin masu garkuwa da mutane, satar shanu, da kuma rikicin makiyaya da manoma sun yiwa ta'addancin Boko Haram a Arewa maso Gabashin Najeriya fintinkau ta fuskar barazana mai munin gaske.

Dan Ali ya yi furucin hakan yayin wani taron karawa juna sani da aka gudanar tsakanin hukumomin tsaro, al'umma da kuma manema labarai a ranar Alhamis, 21 ga watan Maris cikin birnin Kaduna.

Ministan Tsaro; Mansur Dan Ali
Ministan Tsaro; Mansur Dan Ali
Asali: UGC

Akwai bukatar inganta alaka gami da hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da kuma kafofin watsa labarai wajen yakar barazana ta rashin tsaro da ke neman zama ruwan dare a kasar nan kamar yadda Ministan ya zayyana.

KARANTA KUMA: Ku daina bari wasu na rinjayar ku wajen yada rahotanni masu haifar da nakasu ga ci gaban kasa - Buhari ya gargadi 'yan jarida

Minstan ya ce akwai muhimmiyar bukata ta hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da kuma kafofin watsa labarai domin fatattakar miyagu da kuma yakar duk wasu ababe masu haifar da rashin tsaro a Najeriya.

Kazalika shugaban ma'aikatan dakarun soji na Najeriya, Janar Gabriel Olanisakin, ya yi kira na neman hadin kai tsakanin hukumomin tsaro da kuma kafofin watsa labarai da su mike tsaye wajen sauke nauyin da rataya a wuyan su na samar da tsaro tare da kare al'ummar kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel