Ku daina bari wasu na rinjayar ku wajen yada rahotanni masu haifar da nakasu ga ci gaban kasa - Buhari ya gargadi 'yan jarida

Ku daina bari wasu na rinjayar ku wajen yada rahotanni masu haifar da nakasu ga ci gaban kasa - Buhari ya gargadi 'yan jarida

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya shawarci shugabanni da kuma mambobin kungiyar 'yan jarida ta Najeriya, da suka kasance akan yada sahihan rahotanni a ko da yaushe tare da gargadin su akan illolin rahotanni na bogi da shaci fadi.

Ku daina bari wasu na rinjayar ku wajen yada rahotanni masu barazana ga zaman lafiya - Buhari ya gargadi 'yan jarida
Ku daina bari wasu na rinjayar ku wajen yada rahotanni masu barazana ga zaman lafiya - Buhari ya gargadi 'yan jarida
Asali: Facebook

Shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya gargadi 'yan jarida da su daina bari wasu miyagun mutane na rinjayar su wajen yada rahotanni masu cin karo da akidu na zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma.

Shugaban kasar ya yi kiran ne yayin karbar bakuncin kungiyar 'yan jarida ta Najeriya, NUJ, Nigerian Union of Journalists, bisa jagorancin shugaban ta, Mista Chris Isiguzo, da suka ziyarci fadar sa ta Villa da ke garin Abuja a ranar Alhamis, 21 ga watan Maris.

Buhari ya gargadin na neman kawo karshe tare da badda annobar yaduwar rahotanni na bogi a fadin kasar nan masu haifar da barazana ta zaman lafiya gami a kawo nakasun ci gaban kasa ta kowace fuska.

KARANTA KUMA: Mata 31 da Buhari zai yiwa nadin mukamai a sabuwar gwamnatin sa

Kiran na da muhimmanci a halin yanzu kamar yadda shugaban kasa Buhari ya zayyana sakamakon yadda rayuka da dama suka salwanta baya ga asarar dukiya mai tarin yawa a sanadiyar yaduwar rahotanni na bogi.

Ya nemi kungiyar ta 'yan jarida da su hada gwiwa tare da gwamnatin sa wajen bunkasar ci gaban Najeriya tare da inganta alakar ta da sauran kasashen duniya yayin fafutikar kawo karshen annobar yaduwar rahotanni na bogi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel