Zargin magudi da safarar kudi zai kai Emmanuel Jimi gaban Kotu

Zargin magudi da safarar kudi zai kai Emmanuel Jimi gaban Kotu

- Barista Emmanuel Jime ya shiga wani mawuyacin hali a Jihar Benuwai

- Ana karar ‘Dan takarar Gwamnan na APC da laifin awon gaba da kudi

- An maka Mai neman kujerar Gwamnan ne ana daf da yin zaben cike-gibi

Wani babban jigo na jam’iyyar PDP mai mulki a Jihar Benuwai, Terkula Ati, ya shigar da kara har zuwa gaban kotun tarayya da ke zama a Garin Makurdi inda yake zargin Barista Emmanuel Jime da aikata wasu manyan laifuffuka.

Mista Terkula Ati ya shigar da karar ‘dan takarar na APC a jiya Laraba 20 ga Watan Maris ne inda yake neman a damke Emmanuel Jimi, a bincike sa da laifin tafka magudin zabe da kuma safarar wasu makudan kudi kwanaki.

KU KARANTA: Wasu ‘Yan APC sun ce Ministan Buhari ya sa PDP ta ci zaben Gwamna a 2019

Zargin magudi da safarar kudi zai kai Emmanuel Jimi gaban Kotu
Wani babba a PDP ya garzaya da Emmanuel Jimi gaban Alkali
Asali: Facebook

Terkula Ati yana rokon Alkalin kotun da ya bada umarni ga hukumar zabe na INEC mai zaman kan-ta da kuma EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa da su damke Emmanuel Jimi domin a tuhume sa.

Wannan jagora na PDP a Benuwai yana kuma so kotu ta hada da wani Hadimin ‘dan takarar gwamnan mai suna Joseph Manasseh, a wannan bincike. Hakan na zuwa ne daidai lokacin da ake shiryawa zaben cike gibi a Benuwai.

Ati ya fadawa kotu cewa jami’an EFCC da ma’aikatan INEC sun yi ram da ‘dan takarar gwamnan jihar na APC da kuma wannan Hadimi na sa dumu-dumu dauke da kudin da su ka wuce kima da ake ware domin sayen kuri’un jama'a.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel