Rashin Imani: Yadda wani mutumi ya kashe mai juna biyu bayan yayi mata fyade

Rashin Imani: Yadda wani mutumi ya kashe mai juna biyu bayan yayi mata fyade

Rundunar Yansandan jahar Filato ta cafke wani mugun mutumi mai suna Timrimg Napkur wanda take zarginsa da laifin aikata laifin kisan kai akan wata mata mai dauke da juna biyu daya halaka bayan yayi mata fyade, inji rahoton Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mutumin yayi ma matar mai suna Zainab Abu fyade ne a daidai lokacin da taje bakin wani kogi don debo ruwa tare da yaranta biyu mata a kauyn Gangim cikin karamar hukumar Langtang ta kudu.

KU KARANTA: Buhari ya ware naira biliyan 27.4 don daukan nauyin yan gudun hijira

Kwamishinan Yansandan jahar, Isaac Akinmoyede ne ya bayyana haka yayin dayake ganawa da manema labaru a lokacin da hukumar ta bajekolin wanda ake tuhumar da aika mummunan laifi, inda yace bayan ya yi mata fyade sai ya jefata cikin ruwan.

“Da misalin karfe 8 na daren 28 ga watan Feburairu na shekarar 2019, Timrimg dake kauyn Gangnim cikin karamar hukumar Langtang ta kudu ya kai ma wata mat Zainab Abu mai ciki wata bakwai hari a gefen kogi inda taje tare da yayan biyu mata don tayi wanki.

“Wanda ake zargin yayi ma matar fyade, sa’annan ya murde mata wuya, tare da jefata cikin ruwan har sai da ta nutse, ta mutu, yayanta biyu, Aije mai shekaru 7, da Khadija mai shekaru 4 ne suka tsere suka kai rahoto ga mahaifinsu.

“A yanzu haka mun kama wanda ake zargin, kuma ya tabbatar da laifukan daya aikata, sai dai yace yayi da na sanin abinda ya aikata.” Inji kwamishina Akinmoyede. Allah Ya shiga tsakanin nagari da mugu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel