Maimata zabe: Rundunar 'yan sandan jihar Filato ta daura damarar ba sani ba sabo

Maimata zabe: Rundunar 'yan sandan jihar Filato ta daura damarar ba sani ba sabo

Yayin dake ta cigaba da shirye-shiryen gudanar da maimaicin zabukan gwamnonin wasu jahohi a tarayyar Najeriya ranar Asabar mai zuwa, Kwamishinan 'yan sandan jihar Filato ya fitar da kashedi zuwa ga masu son tayar da tarzoma a dukkan fadin jihar.

Kwamishinan 'yan sandan na jihar ta Filato dake a yankin Arewa ta tsakiya, Mista Isaac Akinmoyede shine ya bayyyana hakan a garin Jos, babban birnin jihar yayin da yake fira da manema labarai a ofishin sa.

Maimata zabe: Rundunar 'yan sandan Filato ta dauri damarar ba-sani-ba-sabo
Maimata zabe: Rundunar 'yan sandan Filato ta dauri damarar ba-sani-ba-sabo
Asali: Facebook

KU KARANTA: Sake zabe: Rundunar Sojoji ta gargadi jami'an ta kan katsalandan

Haka ma dai kwamishinan na 'yan sanda yayi anfani da damar wajen yiwa 'yan jaridar baje kolin wasu bata-gari har su 16 da jami'an sa suka kama 'yan kwanakin nan a sassa daban-daban na kasar.

A wani labarin kuma, Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Legas ta sanar da labarin samun nasarar su ta dakile wani shirin sata da wasu barayi suka shirya yi a unguwar Ojo dake a jihar ta Legas.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan ne dai DSP Bala Elkana ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya aike dauke da sa hannun sa zuwa ga manema labarai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel