Hukumar EFCC ta bukaci tsauraran hukunce-hukunce akan barayin man kasar nan

Hukumar EFCC ta bukaci tsauraran hukunce-hukunce akan barayin man kasar nan

Shugaban hukumar nan dake yaki da masu cin hanci da rashawa ta tarayyar Najeriya watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) na rikon kwarya, Ibrahim Magu, ya bukaci a kirkiro wasu sabbin dokoki masu tsauri kan masu satar mai.

Mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Mista Tony Orilade shine ya bayana hakan a cikin wata sanarwar manema labarai da ya aike wa 'yan jarida dauke da sa hannun sa ranar Laraba biyo bayan ziyarar da shugaban hukumar ta EFCC ya kaiwa kwamandan sojojin ruwa, Kwamanda S. Bura a garin Fatakwal.

Hukumar EFCC ta bukaci tsauraran hukunce-hukunce akan barayin man kasar nan
Hukumar EFCC ta bukaci tsauraran hukunce-hukunce akan barayin man kasar nan
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Aisha Buhari ta baiwa 'yan Najeriya shawara kan tarin fuka

Sanarwar ta manema labarai daga Mista Tony ta kuma kara da cewa shugaban na hukumar EFCC ya samu wakilcin shugaban shiyya na hukumar a yankin kudu maso kudancin kasar a garin Fatakwal, Mista Abdulrasheed Bawa.

Mista Abdurasheed Bawa ya kara da cewa yankin na kudancin Najeriya har yanzu yana cikin muhimman shiyyoyi a kasar nan musamman ma ganin cewa daga nan ne ake hako mafi yawan man da kasar ke saidawa domin samun kudin shiga.

A wani labarin kuma, Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Legas ta sanar da labarin samun nasarar su ta dakile wani shirin sata da wasu barayi suka shirya yi a unguwar Ojo dake a jihar ta Legas.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan ne dai DSP Bala Elkana ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya aike dauke da sa hannun sa zuwa ga manema labarai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel