Majalisar dattawa: Okorocha ya bukaci kotu da ta tursasa INEC bashi takardar shaidar cin zabe

Majalisar dattawa: Okorocha ya bukaci kotu da ta tursasa INEC bashi takardar shaidar cin zabe

- Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya bukaci babbar kotun tarayya da ke Abuja, da ta tilasta wa hukumar zabe mai zaman kanta, bashi takardar shaidar cin zaben sanata a yankin Imo ta yamma

- Okorocha yayi korafin cewa INEC ba ta da ikon rike takardar sahidar cin zabensa, inda ya bayyana cewa lallai zabarsa aka yi domin hawa wannan kujera ta sanata

- Justis Taiwo O. Taiwo ya sanya ranar 5 ga watan Afrilu domin fara sauraron lamarin

Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya bukaci babbar kotun tarayya da ke Abuja, da ta tursasa wa hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), bashi takardar shaidar cin zaben sanata a yankin Imo ta yamma.

Okorocha a karar da ya shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/296/2019, yayi korafin cewa INEC ba ta da ikon rike takardar sahidar cin zabensa, inda ya bayyana cewa lallai zabarsa aka yi domin hawa wannan kujera ta sanata.

Majalisar dattawa: Okorocha ya bukaci kotu da ta tursasa INEC bashi takardar shaidar cin zabe
Majalisar dattawa: Okorocha ya bukaci kotu da ta tursasa INEC bashi takardar shaidar cin zabe
Asali: UGC

Ya bukaci kotun da ta kaddamar da cewar abunda hukumar zaben tayi kuskure ne, na kin bashi takardar shaidar cin zabe, duk da cewar Baturen zaben ya kaddamar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

An bayyana INEC a matsayin wacce ake kara a korafin da aka shigar ta tawagar lauyoyinsa karkashin jagorancin Mista Kehinde Ogunwumiju (SAN).

KU KARANTA KUMA: Ko sama ko kasa an nemi Atiku da gwamnoni an rasa a taron gaggawa da PDP ta kira

A halin da ake ciki, Justis Taiwo O. Taiwo ya sanya ranar 5 ga watan Afrilu domin fara sauraron lamarin, duk da cewar ya amince da karar da yan takarar ssanata a jam’iyyun Peoples Democratic Party (PDP), Mista Jones Onyeriri da na All Progressives Grand Alliance (APGA), Sanata Osita Izunaso suka shigar na son shiga shari’ar.

An ambaci Onyeriri da Izunaso a matsayin mutum na biyu da uku a shari’an.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel