Buhari ya ware naira biliyan 27.4 don daukan nauyin yan gudun hijira

Buhari ya ware naira biliyan 27.4 don daukan nauyin yan gudun hijira

Majalisar zartarwa a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu ta amince da kashe kudi naira biliyan ashirin da bakwai da miliyan dari husu (biliyan 27.4) don taimaka ma mutanen da ambaliyan ruwa, rikicin kabilanci da matsalolin tsaro suka daidaita.

Gwamnan jahar Kebbi, kuma mataimakin shugaban majalisar kula da abinci ta Najeriya, Atiku Bagudu ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a fadar gwamnatin Najeriya, a ranar Laraba.

KU KARANTA: Gwamnatin Ganduje tana farautar wani dan jarida ruwa a jallo

Buhari ya ware naira biliyan 27.4 don daukan nauyin yan gudun hijira
Majalisar zartarwar
Asali: Facebook

A jawabinsa, Bagudu yace akalla mutane dubu sittin da tara da dari takwas da saba’in da biyu (69,872) da rikicin addini, na kabilanci da sauran matsalolin tsaro suka addaba ne zasu amfana daga naira biliyan takwas, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Yayin da aka ware naira biliyan goma sha takwas don amfanin mutanen da ambaliyan ruwa yayi ma ta’adi a fadin jahohin Najeriya goma sha hudu, wanda aka kiyatsa adadinsu ga dubu dari da sittin da uku da dari daya da goma sha bakwai (163,117).

Haka zalika gwamnan jahar Kebbi ya bayyana cewa majalisar zartarwa ta amince da bada kwangilar gidan tsangayar ilimin zaman takewa a jami’ar jahar Adamawa akan kudi naira miliyan dari shida da goma sha uku, (613m).

A wani labarin kuma, Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sake kai ziyara jahar Kaduna a watan Maris domin kaddamar da kasuwar duniya ta jahar Kaduna karo na 40, kamar yadda shugaban cibiyar kasuwanci da masana’antu Kaduna, Dakta Muheeba F Dankaba ta bayyana.

Muheeba ta bayyana haka ne yayin wata ziyara da ta jagoranci sauran shuwagabannin cibiyar suka kai zuwa ofishin kamfanin jaridar Daily Trust a babban birnin tarayya Abuja, inda tace sama da kamfanoni 70 daga ciki da wajen kasarnan sun kammala shirin cin wannan kasuwa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel