Yadda wani 'dan sanda ya bindige matashiya har lahira yayin da ya ke cikin maye

Yadda wani 'dan sanda ya bindige matashiya har lahira yayin da ya ke cikin maye

Rahotan da muka samu daga Punch ya nuna cewa wani dan sanda da ya yi tatul da giya a lokacin yana kan aiki ya harbe wata matashiya mai suna Hadijat Sikiru har lahira a unguwar Adamo da ke Ikorodu a jihar Legas a ranar Litinin.

Sai dai a ranar Talata, Rundunar 'yan sandan ta bakin Kakakinta, Bala Elkana ta ce 'yan sandan suna musayar wuta ne da wasu 'yan kungiyar asiri a unguwar Adamo a lokacin da harhashi ta harbe Hadijat kuma wasu 'yan sanda biyu suka jikkata.

Labarin ta dauki sabon salo ne a ranar Laraba a lokacin da majiyar Legit.ng ta ziyarci unguwar Adamo inda wasu shaidun ido su kayi ikirarin cewa 'yan sandan sunyi karya ne domin boye ainihin abinda ya faru.

DUBA WANNAN: Muhawara a kan zaben 2019: Kiris ya rage sanatoci su bawa hammata iska

An shiga farfagaba bayan dan sanda ya harbe matashi haka siddan a Legas
An shiga farfagaba bayan dan sanda ya harbe matashi haka siddan a Legas
Asali: Twitter

Daya daga cikin shaidun, Tope Amusan ya ce dan sandan da ya harbe Hadijat har lahira yana cikin maye kuma bayan ya gano yarinyar ta mutu, ya cika wandonsa da iska domin kada fusatattun mutanen da suka taru suyi masa duka.

Amusan ya ce, "Nayi matukar mamaki bayan na karanta rahoton da 'yan sandan suka bayar a kafafen watsa labarai saboda sun boye gaskiyar lamarin. Dan sandan ne ya kashe yarinyar amma ba haka ce ba.

"Abinda ya faru shine misalin lkarfe 5 na yammacin ranar Litinin mutane suna zaune suna wasa karkashin bishiyar da ke mahadar Adamo inda ake sayar da abinci sai wasu 'yan sanda ya zo cin abinci. Kwatsam sai daya daga cikin 'yan sandan mai lamba 147 a rigarsa ya fito daga shagon mai abincin harba bindigarsa a sama. Hakan ya bawa kowa mamaki saboda babu wata matsala da ke faruwa.

"Na hangi lokacin da shi da abokan aikinsa suke tafiya bayan mintuna 15 sai naji harbin bindiga sau uku. Sai kuma matan da ke sayar da abinci ta fito waje tana ihu cewar dan sandan ya kashe diyarta. Matar ta rike shi amma ya samu ya kubce suka shige motarsu suka tsere."

A lokacin da aka tuntube Kakakin 'yan sanda, Elkana a kan sabon bayanin, ya ce a halin yanzu ana cigaba da bincike kuma idan aka gano dan sandan yana da laifi tabbas zai fuskanci hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel