Tserewar Kanu: Kotu tayi fatali da karar da aka shigar a kan Fani Kayode da Abaribe

Tserewar Kanu: Kotu tayi fatali da karar da aka shigar a kan Fani Kayode da Abaribe

Wata kotun tarayya da ke zamanta a Abuja tayi watsi da karar da aka shigar a kan Sanata Enyinnaya Abaribe da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode game da tserewar shugban haramtaciyar kungiyar masu fafutikan kafa Biyafara, IPOB, Nnamdi Kanu.

Mai sharia John Tsoho ya yi watsi da karar ne saboda rashin bayyana a kotu da lauyan da ya shigar da karar bai yi ba bayan ya shigar da karar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wani lauya mai suna Agidi Ayugu ne ya shigar da kara a kotun inda ya ke bukatar a tilastawa Hukumar 'yan sandan farin kaya, DSS da rundunar 'yan sandan Najeriya su bincike Abaribe da Fani Kayode a kan tserewar Kanu daga Najeriya.

DUBA WANNAN: Muhawara a kan zaben 2019: Kiris ya rage sanatoci su bawa hammata iska

Tserewar Kanu: Kotu tayi watsi da karar da aka shigar a kan Fani Kayode da Abaribe
Tserewar Kanu: Kotu tayi watsi da karar da aka shigar a kan Fani Kayode da Abaribe
Asali: Depositphotos

Sai dai lauyan bai mayar da martani a kan kallubalantar karar da lauyoyin Abaribe da Fani-Kayode su kayi ba a kan karar.

Har ila yau, Ayugu ya bukaci lauyansa, Oghenevo Otemu ya yi karar lauyan Nnmadi Kanu, Ifeanyi Ejiofor da dan uwansa Uchechi Kanu; da kuma wandanda suka karbi belinsa, Tochukwu Uchendu da Emmanuel Shallom-Ben.

Ya yi ikirarin sun da hanna cikin tserewarsa daga Najeriya a watan Satumban 2017 bayan dakarun sojojin Najeriya sun kai sumame gidan iyayen Kanu da ke Afara-Ukwu a garin Umuahia da ke jihar Abia.

Daga baya dai an gano Nnamdi Kanu a faifan bidiyo yana ibada a kasar Isra'ila.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel