Zaben 2019: Abunda ya faru cuta ce karara - Dogara

Zaben 2019: Abunda ya faru cuta ce karara - Dogara

- Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya bayyana zaben 2019 a matsayin cuta karara

- Dogara yace Allah ba zai bar duk mutumin da ya kwaci mulki ta kowani hali ba wai don ya tallafa wa mutane ba

- Kakakin majalisar ya kuma caccaki hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) kan gudanarwar zaben na 2019

Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya bayyana zaben 2019 a matsayin mugunta inda yace duk wadanda suka yi kokarin samun mulki ta kowani hali za su ga makomar su.

Dogara yayi Magana ne a taron gaggawa da kwamitin masu ruwa da tsaki da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) suka kira wanda ya gudana a Wadata Plaza, sakatariyar jam’iyyar na kasa da ke Abuja a ranar Laraba, 20 ga watan Maris.

Zaben 2019: Abunda ya faru cuta ce karara - Dogara
Zaben 2019: Abunda ya faru cuta ce karara - Dogara
Asali: Twitter

Kakakin majalisar ya kuma caccaki hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) kan gudanarwar zaben na 2019.

Dogara ya kuma bayyana cewa duk duk masu son kwace mulki ba wai don su tallafa wa mutane ba za su koyi darasiuinsu.

A nasa bangaren, Shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, ya bayyana cewar nasarar da jam'iyyar APC ke tutiyar ta samu a zabukan da aka kamma ba mai dore wa ba ce.

Shugaban majalisar ya bayyana haka ne jim kadan bayan kammala taron kwamitin zartar wa (NEC) na gaggawa da jam'iyyar PDP ta kira a yau, Laraba, a Abuja.

Saraki ya bayyana cewar sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabrairu asara ce ga kasa baki daya ba iya kawai jam'iyyar PDP ba

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel