Osun 2018: An sa ranar da za a ji wanda ya lashe zaben Gwamna a Kotu

Osun 2018: An sa ranar da za a ji wanda ya lashe zaben Gwamna a Kotu

Mun samu labari cewa Kotun karbar korafin zabe da ke sauraron karar zaben gwamna da aka yi a jihar Osun a cikin Watan Satumban 2018 zai zauna gobe Juma’a 22 ga Watan Maris domin yanke hukunci.

Kotun da ke karbar korafi game da zaben gwamnan jihar Osun zai yi zama ne domin bayyana hukuncin shari’ar da ake yi a gobe. ‘Dan takarar PDP a zaben watau Ademola Adeleke shi ne ya shigar da kara a gaban kotun.

Kwamitin Alkalan nan mutum 3 zai fitar da hukunci ne a Ranar Juma’ar nan a Kotun da ke babban birnin tarayya Abuja bayan sauraron Lauyoyin kowane bangare. Sanata Ademola Adeleke yana kalubalantar nasarar APC a zaben.

KU KARANTA: APC tace Ministan Buhari ya jawo PDP ta doke su a zaben Gwamna

Osun 2018: An sa ranar da za a ji wanda ya lashe zaben Gwamna a Kotu
Kotu za ta yanke hukunci a game da zaben G.Oyetola na APC
Asali: Twitter

Kwamitin na Alkali Ibrahim-Sirajo yace gobe za a sa a san matsayar kotu a game da zaben na jihar Osun. ‘Dan takarar PDP yace an sabawa doka a zaben da ya kawo Gboyega Oyetola, don haka su ka nemi kotu ta sauke sa daga mulki.

Wole Olanipekun shi ne Lauyan da ya tsayawa gwamnan na jam’iyyar APC yayin da babban Lauya Lasco Pwahomdi yake kare hukumar INEC a gaban shari’a. PDP kuma ta dauko hayar Lauya Dr. Onyechi Ikpeazu ne ya kare ta.

Lauyan PDP ya fadawa kotu cewa an yi amfani da kudi wajen sayen kuri’ar jama’a, sannan kuma an tafka magudi da sauran abubuwa domin murde zaben. Lauyoyin da ake tuhuma dai sun nemi ayi watsi da karar idan an zauna a gobe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel