Tanitoluwa Adewumi da Iyayen sa za su gana da Bill Clinton a ofishin sa

Tanitoluwa Adewumi da Iyayen sa za su gana da Bill Clinton a ofishin sa

Mun samu labari cewa tsohon Shugaban kasar Amurka, Bill Clinton, ya gayyaci Tanitoluwa Adewumi da Iyayen sa zuwa ofishin sa da ke cikin Garin Harlem a kasar Amurka bayan ya samu labarin bajintar sa.

Kamar yadda ku ka ji labari kwanaki, Tanitoluwa Adewumi, yaro ne mai shekara 8 da haihuwa kuma ‘Dan asalin Najeriya wanda yayi zarra a wasan nan na Chess a cikin yaran Amurka. Wannan ya labarin sa ya bazu a Duniya.

Bill Clinton yayi wannan jawabi ne a shafin sa na sadarwa na zamani na Tuwita bayan ya ji labarin irin basirar da Ubangiji ya zuba masa. Kyle Griffin ne ya kawo labarin wannan yaro wanda har ta kai ya jawo hankalin Bill Clinton.

KU KARANTA: Hijab: Alkali ya yankewa wata mata hukuncin bulala da daurin shekaru a gidan yari

Bill Clinton wanda yayi mulki a kasar Amurka tsakanin 1993 zuwa 2001 a karkashin jam’iyyar Democrats yayi farin ciki da jin labarin wannan yaro wanda yan ta’addan Boko Haram su ka fatattako Iyayen sa daga Najeriya.

Clinton yake cewa masu zuwa kasar Amurka gudun hijira su na cikin wadanda ke karawa kasar daraja, Clinton ya kara da cewa labarin wannan yaro ‘dan Baiwa ya sa shi farin ciki don haka ya nemi ya zo har ofishin sa su zauna.

Wannan yaro dai yana ta kara samun shahara tun bayan da tsohon shugaban kasar Amurkan ya roki da ya zo ofishin sa. Tanitoluwa Adewumi ya kware ne a wasan Chess inda ya karbi kyauttuka iri-iri a Amurka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel