Za mu cimma hakar danyen mai ganga 2.3m kulli yaumin kamar yadda Buhari ya gabatar - NNPC

Za mu cimma hakar danyen mai ganga 2.3m kulli yaumin kamar yadda Buhari ya gabatar - NNPC

Kamfanin man feturin Najeriya NNPC ta bayyana cewa kamfanin zata cimma manufar hakar danyen man fetur ganga milyan biyu da digo uku kulli yaumin bisa ga kasafin kudin 2019, inda suka bata tabbacin cewa shirya suke don cimma manufar.

Yayinda yake gabatar da jawabi ga kwamitin majalisar dattawa na kudi kan kudaden da ake shirin kashewa tsakanin 2019-2021, dirakta manajan NNPC, Maikanti Baru, ya laburta cewa idan aka kara karfin tsaro a garuruwan da ake samun mai, sunada yakinin cimma wannan manufa.

Diraktan NNPC, wanda manajan shirye-shirye da strateji, Mista Mala Wunti, ya wakilta, ya bayyana cewa duk da cewa Najeriya na da ikon hakar ganganr mai 2.5miliyan kowace rana, rashin tsaro a garuruwan da ake hakan mai ya zamto babban cikas.

KU KARANTA: Bayan zargin da APC sukayi masa, kungiyar lauyoyin Najeriya sun dira kan Singham Wakil

Yace: "Muna godiya, wannan gwamnatin ta shugaba Muhammadu Buhari ta jajrice wajen hada kai da mazauna wadannan garuruwa domin tabbatar da tsaro da ingacin aiki. Wannan zai kara mana karfin gwiwa wajen cimma manufar kasafin kudin 2019."

A kan sharadin kungiyar kasashen da suka fitar da mai kuma (OPEC) kuma, ya bayyana cewa manfuar ganga 2.3milyan ya hada da danyen mai da kuma "condensate', ita OPEC danyen mai kawai ta damu dashi.

Za mu cimma hakar danyen mai ganga 2.3m kulli yaumin kamar yadda Buhari ya gabatar - NNPC
Za mu cimma hakar danyen mai ganga 2.3m kulli yaumin kamar yadda Buhari ya gabatar - NNPC
Asali: Depositphotos

A makon da ya gabata, mun kawo muku cewa kamfanin NNPC ta alanta daukar aiki ga matasa da suka kammala karatun jami'a da kuma wadanda suka fara aiki. Saboda haka duk wanda ke neman aiki ya garzaya shafin yanar gizon "https://www.nnpcgroup.com/career".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel