Yadda yan bindiga suka bude ma Musulmai wuta akan hanyar zuwa Masallaci

Yadda yan bindiga suka bude ma Musulmai wuta akan hanyar zuwa Masallaci

Jama’a Musulmai mazauna rukunin gidajen Aleluya dake cikin garin Osogbo, babban birnin jahar Osun sun gamu da tashin hankali yayin da wasu gungun yan bindiga suka bude musu wuta a daidai lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Masallaci don gudanar da Sallar Asubah.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne da Asubahin ranar Laraba, 20 ga watan Maris, yayin da Musulmai suke gudanar da Sallar Asubahi, kamar yadda wani daga cikin Masallatan ya tabbatar.

KU KARANTA: Tabarbarewar ilimi a Najeriya: Kalli yadda wasu daliban Firamari suke daukan darasi

Yadda yan bindiga suka bude ma Musulmai wuta akan hanyar zuwa Masallaci
Dan bindigan
Asali: UGC

Wani mutumin a wannan Masallaci da ba’a bayyana sunansa ba ya bayyana cewa sun hangi gungun yan bindiga suna biye dasu a baya yayin da suke kan hanyar zuwa Masallaci, daga nan suka shiga kururuwar neman taimako, bayan yan bindigan sun bude musu wuta.

Mataimakin kwamishinan Yansandan jahar, Abu Mustapha ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace ba tare da bata lokaci ba suka aika da jami’an tsaro zuwa inda lamarin ya auku, bayan sun samu rahoto.

Mataimakin kwamishina Abu yace isar Yansanan keda wuya suka mamaye yankin, sa’annan suka samu nasarar kama guda daga cikin yan bindigan, kuma suka kwace bindiga guda daya daga hannunsa.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Osun Folasade Odoro ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda tace tuni Yansanda suka garzaya da dan bindigan daya shiga hannu zuwa ofishin Yansanda dake rukunin gidaje na Dada don bincikensa.

Sai dai babu wani rahoton wanda yan bindigan suka kashe ko ya samu rauni a sakamakon harin, duk kokarin da aka yi na samun wannan bayani daga Yansanda ya ci tura.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel