Hare-haren yan bindiga: Mutan Birnin Gwari suna tserewa daga muhallansu

Hare-haren yan bindiga: Mutan Birnin Gwari suna tserewa daga muhallansu

Wasu mutanen kauye a karamar hukumar Birnin Gwari da jihar Kaduna sun gudu daga muhallansu da gonakinsu sakamakon hare-haren da yan bindiga ke cigaba da kawowa garuruwan da ke makwabtaka da su.

An tattaro cewa mutanen sun gudu daga garuruwan Kamfanin Doka, Goron Dutse, Irirori, Layin Mai Gwari da Kungi zuwa cikin garin Birnin Gwari.

Daya daga cikin manyan garin yace: "Ana kashe mutanenmu kulli yaumin, ana garkuwa da wasu kowace rana, matanmu da yaransu basu tsira ba. Wannan shine dalilin da yasa mutane ke arcewa daga muhallansu domin gujewa wadannan yan bindiga."

"Wadannan mutane sunada abubuwan hawa kuma suna zuwa kauyuka daban-daban suna kai hari cikin kwanciyar hankali. Yan bindigan da suka kashe mutane 15 a ranar Litinin da ya gabata a kauyen Damari, sune suka sake kai hari wasu kauyuka."

Kakakin hukumar yan sandan, Yakubu Sabo, ya ki magana kan al'amarin.

KU KARANTA: Bayan zargin da APC sukayi masa, kungiyar lauyoyin Najeriya sun dira kan Singham Wakil

A baya mun kawo muku rahoton cewa rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutane 17 a harin da wasu ‘yan bindiga su ka kai kauyen Jan Ruwa dake karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

A sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna, DSP Yakubu, ya fitar a yau, Alhamis, ya ce ‘yan bindigar sun saci shanu ma su yawa sun gudu da su bayan kasha mutanen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel