Bayan zargin da APC sukayi masa, kungiyar lauyoyin Najeriya sun dira kan Singham Wakil

Bayan zargin da APC sukayi masa, kungiyar lauyoyin Najeriya sun dira kan Singham Wakil

Kungiyar Lauyoyin Najeriya, shiyar jihar Kano ta bukacin kwamishanan yan sandan jihar, CP Mohammad Wakil wanda akafi sani da Singham, ya nemi gafararta nan da kwanaki biyu kan cin mutuncin mambobinsu yayinda suke ayyukansu na halal.

Sakataren kungiyar, Mujitaba Adamu Amin, a wata jawabi da ya sake ya bayyana yadda wasu jami'an yan sanda kimanin 30 suka garmake mambobin kungiyarsu yayinda suke gudanar da aikinsu.

A cewarsa, yan sandan suna tare da wani dan siyasan Kwankwasiyya sanye da jar hula lokacin da wannan abu ya faru.

KU KARANTA: Uwargidata dukan tsiya take min koda yaushe - Wani Miji ya bayyanawa koTu

Yace: "Wasu jami'an yan sanda rike da makamai kimanin 30 sun ci mutuncin wasu mambobinmu yayinda suke aikin karar zabe; yan sandan na rakiyan wani dan siyasa ne mai sanye da jar hula. Saboda haka, muna magana da babban murya kan wannan abin kunyan da yan sanda sukayi na cin mutuncin mambobinmu."

"Muna kira ga kwamishanan yan sanda ya cire hannunsa daga siyasa kuma ya mayar da hankai kan aikinsa saboda ya fara bayyana cewa abubuwan da shi da yaransa keyi sun fara sabawa dokar kasa da kuma alkawarin da ya dauka."

A baya, jam'iyyar All Progressives Congress APC tana tuhumar kwamishanan yan sandan jihar Kano da zargin hada baki da yan jam'iyyar adawa ta PDP domin kayar dasu a zaben da za'a kammala.

Bayan zargin da APC sukayi masa, kungiyar lauyoyin Najeriya sun dira kan Singham Wakil
Bayan zargin da APC sukayi masa, kungiyar lauyoyin Najeriya sun dira kan Singham Wakil
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel