Yadda INEC tayi min kwangen kuri'u a jihohi 31 - Atiku

Yadda INEC tayi min kwangen kuri'u a jihohi 31 - Atiku

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, ya bayyana cewar bayanan daga daga na'urar hukumar zabe ta kasa (INEC) sun nuna yadda aka rage ma sa kuri'u a zaben shugaban kasa a jihohi 31 da birnin tarayya, Abuja.

Atiku ya bayyana hakan ne a cikin takardar karar da ya shigar gaban koton sauraron korafe-korafe a kan zaben shugaban kasa.

Dan takara na PDP ya bayyana cewar ya kayar da shugaba Buhari da tazarar kuri'u 1,615,302.

Ya ce na'urar hukumar INEC ta nuna cewar ya samu adadin kuri'u 18,356,732 da suka bashi rinjaye a kan shugaba Buhari, wanda ya samu kuri'u 16,741,430.

A ranar 27 ga watan Fabrairu ne hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana shugaba Buhari na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar shugaban kasa.

A sanarwar INEC ta bakin shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shugaba Buhari na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 15,191,847 yayin da babban abokin hamayyar sa, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 11,262,978.

Yadda INEC tayi min kwangen kuri'u a jihohi 31 - Atiku
Atiku
Asali: Depositphotos

Atiku ya ce na'urar tantance masu zabe na aika sakamakon zabe daga kowacce akwati zuwa babbar na'urar hukumar INEC.

Ya kara da cewa INEC ta fitar da adadin mutanen da ta yiwa rijista kafin zabe amma kuma ta shigar da wani adadi na daban a fom din EC8D(A)

Atuku ya ce a jihar Abia ya samu kuri'u 664,659 kamar yadda na'urar INEC ta nuna amma INEC ta rubuta ya samu kuri'u 219,698.

A jihar Adamawa ya ce kuri'u 646,080 ya samu ba 410,266; a Akwa Ibom ya ce ya samu kuri'u 587,431 sabanin 395,832 da INEC ta rubuta; a Anambra kuri'u 823, 668 sabanin of 524,738; a jihar Bayelsa ya samu kuri'u 332, 618 sabanin 197, 933; a jihar Benue kuri'u 529,970 ya ce ya samu ba 356, 817 da INEC ta bayyana ba; a jihar Borno kuri'u 281,897 sabanin kuri'u 71, 788; a jihar Kuros Riba ya ce kuri'u 572, 220 ya samu ba kuri'u 295, 737 da INEC ta bayyana ba.

DUBA WANNAN: Babu tabbacin gudanar da zaben kece raini a jihar Adamawa - INEC

A ragowar jihohin, Atiku ya ce ya samu kuri'u 778,369 a jihar Delta, sabanin 594, 068; a Ebonyi 565, 762 sabanin 258, 573; a Edo 677,937 sabanin 275,691; a Enugu 698,119 sabanin 355,553; a Abuja 419,724 sabanin 259,997; a Gombe 684,077 sabanin 138,484; a Imo 485,627 sabanin 334,923; a Jigawa 539,522 sabanin 289,895; a Kaduna 961,143 sabanin 649,612; a Kano 522,889 sabanin 391,593; a Katsina kuma ya ce kuri'u 160,203 ya samu.

A Kebbi 493,341 sabanin 154,282; a Kogi 504,308 sabanin 218,207; a Kwara 353,173 sabanin 138,184; a Lagos 1,103,297 sabanin 448,015; a Nasarawa 344,421 sabanin 283,847; a Neja 576,308 sabanin 218,052; a Ogun 438,099 sabanin 194,655; a Ondo 451,779 sabanin 275,901; a Oyo 527,873 sabanin 366,690; a Sokoto 552,172 sabanin 361,604; a Taraba 442,380 sabanin 374,743; a Yobe 306,841 sabanin 50,763 sai Zamfara da ya ce ya samu kuri'u 379,022 sabanin 125,123.

Kazalika, ya bayyana cewar INEC ta kara masa yawan adadin kuri'un da ya samu a jihohin Osun da Filato.

Ya ce a jihar Osun ya samu kuri'u 337,359 kamar yadda na'urar INEC ta nuna amma sai hukumar ta rubuta ya samu 33,377, yayin da a jihar Filato ya ce kuri'u 273,031 ya samu kamar yadda na'ura ta nuna ba kuri'u 548,665 da INEC ta bayyana ba yayin tattara sakamako.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel