Nasarar da kuke tutiya da ita ba mai dorewa ba ce - Saraki ya fada wa APC

Nasarar da kuke tutiya da ita ba mai dorewa ba ce - Saraki ya fada wa APC

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, ya bayyana cewar nasarar da jam'iyyar APC ke tutiyar ta samu a zabukan da aka kamma ba mai dore wa ba ce.

Shugaban majalisar ya bayyana haka ne jim kadan bayan kammala taron kwamitin zartar wa (NEC) na gaggawa da jam'iyyar PDP ta kira a yau, Laraba, a Abuja.

Saraki ya bayyana cewar sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabrairu asara ce ga kasa baki daya ba iya kawai jam'iyyar PDP ba.

A ranar 27 ga watan Fabrairu ne hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana shugaba Buhari na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar shugaban kasa.

A sanarwar INEC ta bakin shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shugaba Buhari na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 15,191,847 yayin da babban abokin hamayyar sa, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 11,262,978.

Nasarar da kuke tutiya da ita ba mai dorewa ba ce - Saraki ya fada wa APC
Bukola Saraki
Asali: Depositphotos

Sai dai a jawabinsa bayan INEC ta sanar da sakamakon zaben, Atiku ya bayyana cewar zai ta fi kotu domin kalubalantar nasarar da shugaba Buhari ya samu tare da bayyana cewar an tafka magudi yayin zaben.

A jawabinsa na yau, Saraki ya bayyana cewar zaben shugaban kasar da aka gudanar ya mayar da Najeriya abar dariya a idon duniya, kuma kamata ya yi wadanda aka bayyana sun yi nasara su ji kunya ba suke murna ba.

"Wannan nasarar da suke tutiyar sun samu ba mai dorewa ba ce. Duk wanda yake ganin PDP ce bata samu nasara ba ya kamata ya canja tunani, don kuwa Najeriya bata samu nasara ba

DUBA WANNAN: Yadda APC tayi amfani da sojoji wajen tafka magudi - Buba Galadima

"Babban abin kunya shine gudanar da zaben da a matsayin mu na kasa ba zamu iya alfahari da shi ba.

"Mu ne muka gudanar da zabe na gaskiya da kowa ya gamsu da shi amma irin wannan zaben da suka yi abin kunya ne ga su kansu.

"Ba jam'iyyar PDP ce tayi rashin nasara ba, rashin nasarar na Najeriya ne. Ina da karfin guiwar cewar wannan nasarar da suka gadara da ita ba zata dore ba. A saboda haka nake kira ga jama'ar da za a gudanar da zabe a zagaye na biyu a jihohinsu da su fita domin kada kuri'unsu ga jam'iyyar PDP tare da yin kira ga INEC da su tabbatar sun yi gaskiya a wannan karon," a cewar Saraki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel