Tarin fuka: Aisha Buhari ta baiwa 'yan Najeriya muhimmiyar shawara

Tarin fuka: Aisha Buhari ta baiwa 'yan Najeriya muhimmiyar shawara

Uwar gidan shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari ta shawarci 'yan Najeriya da su rika zuwa gwajin cutar nan ta tarin fuka akai akai domin sanin matsayi da kuma neman magani idan tsautsayi ya gitta.

Uwar gidan Shugaban kasar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar manema labarai da rarraba a ranar Laraba ta bayyana cewa alamomin cutar ta tarin fuka sun hada da yin tari ba kakkautawa har na tsawon sati biyu a jere.

Tarin fuka: Aisha Buhari ta baiwa 'yan Najeriya muhimmiyar shawara
Tarin fuka: Aisha Buhari ta baiwa 'yan Najeriya muhimmiyar shawara
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta shirya siyar da hannun jarin Naira biliyan 100

Ita dai Aisha Buhari ita ce Ambasadan wata kungiya da dake yaki da cutar tarin fukar kuma tana anfani da matsayin na ta wajen isar da sakon da ya shafi cutar ga al'umma.

A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar garin Abuja, babban birnin tarayya sun bayyana samun nasarar cafke wata mata mai suna Aisha Bello mai shekaru 37 a duniya bisa ga laifin badda-kama da sunan uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari.

Yayin da yake bayyana matar ga manema labarai jiya a Abuja, kwamishinan 'yan sandan garin na Abuja, Sadiq Bello ya bayyana cewa ita matar ta kware ne wajen yin anfani da sunan Aisha Buhari din don ta damfari al'umma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel