Buhari ya kafa kwamitin bitar aiyuka da tsare-tsaren gwamnatin sa

Buhari ya kafa kwamitin bitar aiyuka da tsare-tsaren gwamnatin sa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa wani kwamiti da zai yi bitar aiyuka da tsare-tsaren gwamnatinsa a shekaru hudu da suka gabata. Kwamitin da farfesa Yemi Osinbajo, mataimakain shugaban kasa, ke jagoranta zai zakulo nasara ko akasin haka da gwamnati ta samu a shekaru hudu na farko.

Fadar shugaban kasa ce ta sanar da hakan a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Tuwita a yau, Laraba.

Sanarwar ta bayyana cewar shugaba Buhari ya kafa kwamitin ne domin samun alkibla a kan irin bangarorin da gwamnati ya kamata ta yi gyare-gyare ko garambawul ko kuma bawa fifiko a shekaru hudu da zata yi a zango na biyu.

A yayin da Buhari ke kafa kwamiti domin tunkarar zango na biyu, shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, ya bayyana cewar nasarar da jam'iyyar APC ke tutiyar ta samu a zabukan da aka kamma ba mai dore wa ba ce.

Buhari ya kafa kwamitin bitar aiyuka da tsare-tsaren gwamnatin sa
Buhari da Osinbajo
Asali: Facebook

Shugaban majalisar ya bayyana haka ne jim kadan bayan kammala taron kwamitin zartar wa (NEC) na gaggawa da jam'iyyar PDP ta kira a yau, Laraba, a Abuja.

Saraki ya bayyana cewar sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabrairu asara ce ga kasa baki daya ba iya kawai jam'iyyar PDP ba.

DUBA WANNAN: Babu tabbacin gudanar da zaben kece raini a jihar Adamawa - INEC

A ranar 27 ga watan Fabrairu ne hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana shugaba Buhari na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar shugaban kasa.

A sanarwar INEC ta bakin shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shugaba Buhari na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 15,191,847 yayin da babban abokin hamayyar sa, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 11,262,978.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel