Sata-tayi-gardama: 'Yan sanda sun kama barayi 2, sun kashe 1 a Legas

Sata-tayi-gardama: 'Yan sanda sun kama barayi 2, sun kashe 1 a Legas

Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Legas ta sanar da labarin samun nasarar su ta dakile wani shirin sata da wasu barayi suka shirya yi a unguwar Ojo dake a jihar ta Legas.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan ne dai DSP Bala Elkana ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya aike dauke da sa hannun sa zuwa ga manema labarai.

Sata-tayi-gardama: 'Yan sanda sun kama barayi 2, sun kashe 1 a legas
Sata-tayi-gardama: 'Yan sanda sun kama barayi 2, sun kashe 1 a legas
Asali: Twitter

KU KARANTA: Buhari yayi fatali da kudurorin doga 2 daga majalisa

A cewar sa, wasu mazauna unguwar ta Ojo ne suka kai korafi a ofishin 'yan sandan unguwar game da shirin na barayin inda su kuma jami'an su suka daura damara suka kuma tunkare su har Allah ya basu nasara akan su.

Ya kara da cewa a yayin artabun na su, 'yan sandan sun yi nasarar bingige daya daga cikin barayin sannan kuma suka kama wasu biyu daga cikin su.

A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayya ta hada tare da tura wata rundunar hadin gwuiwa ta kwararrun jami'an sojoji da 'yan sanda a kauyen Nandu Gbok dake a karamar hukumar Sanga, jihar Kaduna domin kwantar da tarzoma inda wasu 'yan bindiga suka kashe mutane 9 da kona gidaje 30.

Rundunar hadin gwuiwar dai ta bayar da tabbacin samar da zaman lafiya tabbatacce a kauyen da ma sauran garuruwan jihar tare da kamo wadanda suka aikata laifin domin gurfanar da su gaban alkali don fuskantar shari'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel