Muhawara a kan zaben 2019: Kiris ya rage sanatoci su bawa hammata iska

Muhawara a kan zaben 2019: Kiris ya rage sanatoci su bawa hammata iska

Anyi hayaniya sosai a zauren majalisar dattawa yayin zaman da akayi na yau Laraba 20 ga watan Maris a lokacin da ake tattaunawa a kan zargin da wasu keyi na cewa anyi amfani da sojoji fiye da kima a wasu jihohi yayin zaben 2019.

Sanata Dino Melaye mai wakiltan Kogi ta Yamma a majalisar ne ya gabatar da kudirin zargin amfani da sojoji fiye da kima a lokacin zaben da kuma zargin fifiko da Hukumar Zabe INEC ta aikata a wasu johohin a cewarsa.

Wasu sanatoci bakwai da suka hada da Sanata Mao Ohabunwa (Abia ta Arewa), Samuel Anyanwu (Imo ta Gabas), Ahmed Ogembe (Kogi ta Tsakiya), Obinna Ogba (Ebonyi ta Tsakiya), Matthew Uroghide (Edo ta Kudu), Clifford Ordia (Edo ta tsakiya) Biodun Olujimi (Ekiti ta Kudu) duk sun goyi bayan Dino Melaye.

Muhawara a kan zaben 2019: Kiris ya rage sanatoci su bawa hammata iska
Muhawara a kan zaben 2019: Kiris ya rage sanatoci su bawa hammata iska
Asali: Facebook

Kamar yadda ya ke cikin kudirin, 'yan majalisar sun bayyana damuwarsu a kan abinda suka kira amfani da sojoji fiye da kima da kuma son kai da INEC ta ke nunawa wurin zartar da dokoki mabanbanta a zabukan da aka gudanar yana barazana ga demokradiyar Najeriya.

DUBA WANNAN: Buhari ya yi watsi da wasu kudiri 5 da majalisa ta amince da su

Mahawara tsakanin sanatocin da ke goyon bayan kudirin na Dino Melaye da kuma wadanda ba su amince da ita ba tayi zafi sosai inda suka rika yiwa junansu ihu har ta kai ga an kusa a fara dambe amma sai shugabab Majalisa Bukola Saraki ya shiga tsakani.

Bayan an dauki lokaci mai tsawo ana tafka muhawara a kan batun, majalisar da cimma matsayar yin Allah wadai da amfani da sojoji fiye da kima lokacin zabe kana ta kuma bukaci INEC ta tabbatar da cewa ba ta nuna banbanci wurin zartar da dokokinta.

Majalisar ta kuma bukaci kwamitin majalisar na INEC ta gudanar da bincike a kan zargin nuna fifiko da aka ce INEC tayi wurin zartar da dokokin zabe yayin zaben na 2019.

Majalisar ta kuma yi kira da Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da kudirin yiwa dokar zabe kwaskwarima domin tabbatar da adalci tsakanin 'yan takara da kuma karfafa demokradiyar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel