Shari'ar Maryam Sanda ya tsaya cik: Alkali ya ki zuwa kotu

Shari'ar Maryam Sanda ya tsaya cik: Alkali ya ki zuwa kotu

Rashin zuwan Alkali mai shari'a ya tsayar da shari'ar Maryam Sanda wace ake tuhuma da zargin kisan mijinta, Bilyaminu Bello, cik a ranar Laraba, 20 ga watan Maris, 2019.

Maryam Sanda na gurfana gaban babban kotun birnin tarayya dake Maitama kan zargin kisan mijinta, wanda dan uwa ne ga tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Alhaji Bello Halliru Mohammad.

An gurfanar da ita ne tare da dan uwanta, Aliyu Sanda, da mahaifiyarta, Maimuna Aliyu da kuma mai aikinus, Sadiya Aminu, bisa ga zargin taimaka mata wajen boye gaskiya ta hanyar goge jinin mamacin bayan bayan abinda ya faru. Amma sun musanta hakan.

A bayan lauyan Maryam Sanda ya shigar da bukata gaban kotun cewa lauyan gwamnati ba tada isassun hujjojin da suka nuna cewa Maryam Sanda ta aikata laifin. Idan Alkali ya karbi wannan bukata, za'a saketa ta tafi. Amma idan Alkalin ya kiya, za'a bukaceta ta kare kanta.

Kotun ta daga karar zuwa ranar 20 ga watan Maris domin sauraronsu. Amma yayinda suka isa kotu, sun samu cewa alkalin, Jastis Halilu Yusuf, bai zo kotu ba.

A yanzu dai an dakatad da karan zuwa ranar 26 ga watan Maris, 2019.

KU KARANTA: Da alamun PDP da Atiku sun shiga dimuwa - Martanin APC kan ikirarin cewa Atiku lallasa Buhari da kuri'u 1.6m

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel