Da alamun PDP da Atiku sun shiga dimuwa - Martanin APC kan ikirarin cewa Atiku lallasa Buhari da kuri'u 1.6m

Da alamun PDP da Atiku sun shiga dimuwa - Martanin APC kan ikirarin cewa Atiku lallasa Buhari da kuri'u 1.6m

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana cewa ga dukkan alamu, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta, Alhaji Atiku Abubakar, sun shiga wani bala'in dimuwa sakamakon fadin da sukayi a zabe.

APC ta bayyana hakan ne yayinda take martani kan ikirin PDP cewa dan takararta, Atiku Abubakar, ya lallasa shugaba Muhammadu Buhari da kuri'u miliyan daya da dubu dari shida.

Kakakin jam'iyyar APC, Malam Nasir Issa-Onilu ya bayyana cewa: "Yayinda muna sane kwarai da kaidin PDP na kokarin bata zaben shugaban kasan da ya gudana, inda masu lura da zabe a gida da wajen Najeriya suka shaida, muna masu jajintawa Atiku kan muguwar kayi da ya sha a hannun shugaba Buhari ta kuri'un yan Najeriya."

"Dubi ga irin kalaman da ke fitowa daga bakin Atiku da PDP a kwanakin nan, ya bayyana cewa sun shiga dimuwa mai karfi da kuma maye."

"Bayan makonni suna sama da kasa, PDP ta farka daga baccinta bayan irin kayin da ta sha kuma ta garzaya kotun zabe domin shigar da kara. Amma cikin dukkan tuhume-tuhumen da ya gabatar a kotu maras inganci, mafi takaici shine na cewa na'urar tattara sakamakon INEC ya nuna cewa shi ya lashe zaben da kuri'u 1.9 miliyan."

"Tambayoyi kadan zamu tanbayesu - shin wannan kuri'u 1.6million, a Dubai aka samosu? Shin bokaye Atiku suka sayar masa?."

KU KARANTA: Atiku kuri'u 18,356,732 ya samu yayinda Buhari ya samu 16,741,430 - Lauyoyin PDP

Issa-Onilu ya kara da cewa yadda PDP ke yawan ambatan na'urara tattara kuri'un INEC, da alamun cewa sun yi kokarin katsalandan amma Allah bai basu dama ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel