'Yan sanda sun kama magidancin da ya kashe saurayin matar sa

'Yan sanda sun kama magidancin da ya kashe saurayin matar sa

Rundunar 'yan sanda reshen jihar Ogun ta sanar da cewar ta kama wani magidanci mai shekaru 25 bisa aikata laifin kisan wani mutum, Olakitan Balogun, da ya zargi da kulla alaka irinta soyayya da matar sa.

A cikin jawabin da ta fitar ta ofishin Mista Abimbola Oyeyemi, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Ogun, rundunar ta ce sun kama magidancin ne da misalin karfe 1:45 na daren ranar Lahadi.

Sanarwar ta kara da cewa ta yi nasarar kama magidancin ne bayan samun kira daga wasu makwabtan gidan da lamarin ya faru a rukunin giaje na Doland.

"DPO na ofishin 'yan sanda dake Ajuwon bai bata lokaci ba wajen jagorantar jami'an 'yan sanda zuwa inda abin ya faru, kuma nan take suka kama wanda ake zargi da aikata kisan.

"Wanda ake zargin ya shaida mana cewar ya kashe mutumin da yake zargi na soyayya da matar sa bayan ya dawo gida ya same shi tare da matar sa da misalin karfe 12:30 na dare.

'Yan sanda sun kama magidancin da ya kashe saurayin matar sa
'Yan sanda
Asali: Facebook

"Hakan ne ya fusata shi har ta kai ga ya buga kan mutumin da jikin bango, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar sa," a cewar jawabin.

Sai dai a nata jawabin, matar magidancin ta musanta cewar tana da wata alakar soyayya da marigayin.

DUBA WANNAN: Maimaita zabe: Rundunar sojin sama ta fara jigilar kayan aiki zuwa jihohi

A cewar jawabin da matar ta bawa rundunar 'yan sanda ta bayyana cewar mijin nata ya kaurace ma ta na tsawon wata 8 amma kuma duk da haka ya saka maigadi ya ke sa ido, ya sanar da shi duk lokacin da ya gan ta tare da wani namiji.

Ta kara da cewa marigayin ya kawo ma ta ziyara ne tare da budurwar sa domin su gaisa kasancewar akwai zumunci tsakaninsa da iyalin ta.

Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewar ta kai gawar marigayin dakin ajiyar gawa yayin da take cigaba da gudanar da bincike a kan mai laifin kafin ta gurfanar da shi a gaban kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel