Zagaye na biyu: Rundunar sojin Najeriya ta gargadi jami'an ta kan katsalandan

Zagaye na biyu: Rundunar sojin Najeriya ta gargadi jami'an ta kan katsalandan

Rundunar sojojin Najeriya ta gargadi jami'an ta akan yin katsalandan a harkokin zabukan da za'a sake gudanarwa na zagaye na biyu na gwamnonin wasu jahohin Najeriya ranar Asabar din nan da take tafe.

Kwamandan rundunar sojojin ta shiyyar ta 8 dake jihar Sokoto Hakeem Otiki ne ya bayyana hakan ranar Larabar nan yayin da yake jawabi ga dakarun rundunar tare da fadakarwa akan harkokin zaben.

Zagaye na biyu: Rundunar sojin Najeriya ta gargadi jami'an ta kan katsalandan
Zagaye na biyu: Rundunar sojin Najeriya ta gargadi jami'an ta kan katsalandan
Asali: Facebook

KU KARANTA: Zaben 2019: Abun da ya sa muka tafi kotu - Obi

A cewar kwamandan dole ne jami'an rundunar sojin kasar su tabbata sun bayyana kyakkyawar alakar su ga farar hula domin tabbatuwar mutunci da kimar rundunar a idon duniya baki daya.

A wani labarin kuma, hukumar gwamnatin tarayyar Najeriya dake da alhakin tattara haraji ta kasa watau Federal Inland Revenue Service (FIRS) a ranar Talata ta bukaci 'yan Najeriya da su kwana da shirin ko-ta-kwana na karin harin kayayyaki a shekarar nan ta 2019.

Hukumar ta FIRS ta bayyana cewa tana nan tana shirye-shiryen yin karin harajin na bangaren da ake kira da Value Added Tax (VAT) da kaso 35 zuwa 50 cikin dari domin samar da kudaden shigar da za a iya dabbaka kasafin kudin na 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel