Da duminsa: El-Rufa'i ya karyata masu jita-jita, ya dawo gida da lafiyarsa

Da duminsa: El-Rufa'i ya karyata masu jita-jita, ya dawo gida da lafiyarsa

Mai magana da yawun gwamnan jihar Kaduna, Samuel Aruwa, ya bayyana yadda Malam Nasir El-Rufa'i ya kunyata masu yada jita-jita akansa cewa ya samu hadari kuma ya mutu jim kamdan bayan nasarar da ya samu a zaben 9 ga watan Maris, 2019.

Samuel Aruwan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook inda ya yayi isgili ga masu yada wannan karya da cewa, shin sai me kuma?

Yace: "Mai yawan fara'a gwamna Nasir El-Rufa'i a babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe, Abuja. Wani jita-jita kuma ya rage?"

Da duminsa: El-Rufa'i ya karyata masu jita-jita, ya dawo gida da lafiyarsa
Da duminsa: El-Rufa'i ya karyata masu jita-jita, ya dawo gida da lafiyarsa
Asali: Facebook

KU KARANTA:

Za ku tuna cewa jita-jita ta yadu musamman a kafofin ra'ayi da sada zumunta cewa gwamna Kaduna ya samu hadari kuma yana cikin halin ni 'yasu. Ba tare da bata lokaci ba, gwamnan ya karyata maganar amma duk da haka ba'a daina ba saboda an kwana biyu ba'a ganeshi ba.

Yace: "Na tashi bayan baccin sa'o'i 8 kawai sai na samu labarin wasu yan bakin ciki, ya PDP masu yada labarin karya suna alanta cewa direba ya mutu kuma ina cikin halin ni 'yasu."

"Wannan duka karya ne. Na gode musu da kara mini yawan kwana ta hanyar rage nasu. Ban gushe babban abun tsoronsu ba kuma ba zan gushe ba har sai na gama musu ritaya idan Allah ya yarda kuma an biznesu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel