Maimaita zabe: Rundunar sojin sama ta fara jigilar kayan aiki zuwa jihohi

Maimaita zabe: Rundunar sojin sama ta fara jigilar kayan aiki zuwa jihohi

A yau, Laraba, ne shugaban rundunar sojin sama ta kasa (CAS), Air Marshall Sadique Abubakar, ya bayyana cewar rundunar sojin sama ta fara jigilar kayan aikin zabe zuwa jihohin da za a sake maimaita zaben gwamna ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

Ya bayyana hakan ne yayin wani taro da manyan kwamandojin rundunar sojin sama da ake yi duk bayan wata uku a hedikwatar rundunar sojin sama (NAF) da ke Abuja.

"Dangane da batun maimaita zabe a wasu jihohi, jiragen mu sun kai wasu kayan aikin zabe zuwa Jalingo, Yola da Bauchi a jiya.

"Zamu karasa jigilar kayan aikin zabe zuwa dukkan inda hukumar zabe ta kasa (INEC) ke bukatar mu kai ma su," a cewar Abubakar.

Ya kara da cewa NAF ta samu nasarar jigilar kayan aikin zabe da nauyin su ya kai kilogiram 820,000 zuwa sassan kasar nan daban-daban.

Maimaita zabe: Rundunar sojin sama ta fara jigilar kayan aiki zuwa jihohi
Rundunar sojin sama ta fara jigilar kayan aiki zuwa jihohi
Asali: Twitter

"Mun yi nasarar kammala jigilar kayan aikin zabe a lokacin zaben shugaban kasa da na mambobin majalisar tarayya da kuma na gwamnoni da 'yan majalisar dokoki duk da kasancewar an shigo da mu cikin aikin rabon kayan a kurarren lokaci," a kalaman Abubakar.

DUBA WANNAN: Yadda APC tayi amfani da sojoji wajen tafka magudi - Buba Galadima

Ya mika godiyar sa ga direbobin rundunar NAF da ayarin injiniyoyi da suka tabbatar da samun nasarar kammala jigilar kayan aikin zabe a kan lokaci.

Kazalika, ya bayyana cewar NAF na saka ran karbar wasu sabbin jirage masu saukar ungulu da shugaba Buhari ya sayo daga kasar Italy.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel