Fayose a kotu: Ban da wata shaida akan kan zargin da ake yi wa Fayose - Tsohon minista

Fayose a kotu: Ban da wata shaida akan kan zargin da ake yi wa Fayose - Tsohon minista

Daya daga cikin shiadu da suka yi sheida akan zarge-zargen da ake yi wa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose kuma tsohon karamin ministan tsaro a gwamnatin shugaba Jonathan, Musiliu Obanikoro ya ce ba ya da wata shaida ta takarda akan abunda ya ce a gaban kotun.

Shi dai Obanikoro na zaman shaida ta biyar da hukumar EFCC ta gabatar a kotu yayin cigaba da take yi da tuhumar tsohon gwamnan na Ekiti akan zargin wawure kudaden gwamnatin jihar sa lokacin da yana gwamna.

Fayose a kotu: Ban da wata shaida akan kan zargin da ake yi wa Fayose - Tsohon minista
Fayose a kotu: Ban da wata shaida akan kan zargin da ake yi wa Fayose - Tsohon minista
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hamid Ali ya yi sabbin nade-nade

Sai dai bayan ya kammala bayar da sheidar ta sa, sai Lauyan dake kare bangaren wadanda ake tuhuma, Mista Olalekan Ojo (SAN) ya tambaye shi ke yana iya tabbatar da bayanan da yayi a gaban kotun inda shi kuma ya ce a'a.

A wani labarin kuma, Hukumar gwamnatin tarayyar Najeriya dake da alhakin tattara haraji ta kasa watau Federal Inland Revenue Service (FIRS) a ranar Talata ta bukaci 'yan Najeriya da su kwana da shirin ko-ta-kwana na karin harin kayayyaki a shekarar nan ta 2019.

Hukumar ta FIRS ta bayyana cewa tana nan tana shirye-shiryen yin karin harajin na bangaren da ake kira da Value Added Tax (VAT) da kaso 35 zuwa 50 cikin dari domin samar da kudaden shigar da za a iya dabbaka kasafin kudin na 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel