Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Laraba, 20 ga watan Maris ya soki ikirarin jami’ar National Open University of Nigeria (NOUN) na cewa suna biyansa alawus kowace shekara na rawar ganin da yake takawa a matsayin wani malami a jami’ar.
Cif Olusegun Obasanjo, ya kasance daya daga cikin malamai ma su horar da dalibai a jami'ar NOUN reshen ta na jihar Ogun.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Shugaban jami'ar ya bayyana cewa Obasanjo na karban N40,000 a matsayin albashi, yayin ganawa da manema labarai, inda ya bayar da tabbacin yadda a halin yanzu tsohon shugaban kasa ke kulawa tare da horas da wasu dalibai biyu a fannin nazarin Tauhidin addinin Kirista da ya kasance mai digirin digirgir a fannin.

Obasanjo ya musanta karbar albashi daga NOUN
Source: UGC
Sai dai tsohon Shugaban kasar yace ko taro bau taba karba ba a matsayin albashi daga jami’ar, don haka ya nemi Shugaban makarantar ya roke shi gafara wakan wannan kage da yayi masa.
KU KARANTA KUMA: Albashin N40,000 Obasanjo ya ke dauka a kowace shekara - Farfesa Adam
Ya bayyana cewa furucin Shugaban jami’ar cin fuska ne a gare shi domin lamarin ya janyo cece-kuce a fadin duniya. Saboda haka ya neman Shugaban makarantar ya janye kalamansa sannan ya nemi yafiyarsa.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta: