Majalisa za ta yi kokari ta gama aiki a kan kasafin kudi a watan nan - Saraki

Majalisa za ta yi kokari ta gama aiki a kan kasafin kudi a watan nan - Saraki

Jaridar Leadership ta rahoto cewa majalisar dattawa da ta wakilan tarayya su na cigaba da kokarin ganin sun kammala aikin da ya dace a kan kasafin kudin shekarar bana na 2019 zuwa farkon watan gobe.

Majalisun tarayyar za su dage wajen ganin sun gama duk wata zama da za ayi a kan kundin kasafin kudin Najeriya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo gaban su tun a karshen bara. Ana sa rai a batar da Tiriliyan 8.83 a bana.

A zaman da ‘yan majalisar su kayi jiya, muhawarar da ake yi a game da kundin kasafin kudin na Najeriya ya kai zuwa mataki na gaba. Yanzu dai har ta kai Sanatoci sun cin ma matsayar cewa za su yi kokarin gama duk aikin da ya dace.

KU KARANTA: Shugaba Buhari na shirin saida hannayen jari na Naira biliyan 100

Majalisa za ta yi kokari ta gama aiki a kan kasafin kudi a watan nan - Saraki
‘Yan Majalisa sun kusa gama aiki a kan kasafin kudin bana
Asali: UGC

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki yake cewa kwamitin da ke lura da harkar kasafin kasar za tayi aikin ta, sannan ta kawowa majalisa rahoto a Ranar 2 ga Watan Afrilu. Bukola Saraki yace ana sa rai a ranar za a tike aikin kasafin.

Idan dai an dace za a iya karasa duk aikin da ya rage a kan kasafin na bana ne a farkon Watan na Afrilu. A daidai wannan lokaci kuma za a dage wajen ganin shugabannin hukumomin gwamnati na MDA sun kare kasafin su a majalisar.

A majalisar wakilai ma dai labarin duk daya ne inda shugabannin majalisar su ka roki ‘yan uwan su da su karkare duk abin da ya dace a cikin wannan watan. Hakan zai bada dama ‘yan majalisar su gama komai a cikin farkon Afrilun gobe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel