Gwamanatin tarayyar Najeriya za ta sayar da hannayen jari na Naira biliyan 100

Gwamanatin tarayyar Najeriya za ta sayar da hannayen jari na Naira biliyan 100

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana kudurin ta na tatsar kudi daga 'yan Najeriya ta hanyar sayar da wasu hannayen jari ga 'yan kasar har na Naira biliyan 100 a ranar 27 ga watan Maris, kamar dai yadda ofishin kula da basussuka na kasa, Debt Management Office (DMO) ya bayyana.

Ofishin na DMO ne dai ya bayar da wannan sanarwar a wani kundi da suka wallafa a shafin yanar gizon su ranar Talata da ta gabata a garin Abuja.

Gwamanatin tarayyar Najeriya za ta sayar da hannayen jari na Naira biliyan 100
Gwamanatin tarayyar Najeriya za ta sayar da hannayen jari na Naira biliyan 100
Asali: UGC

KU KARANTA: Za'a kara kudin haraji a Najeriya - FIRS

Sanarwar ta DMO ta bayyana cewa hannayen jarin na Naira biliyan 40 za su balaga ne su isa siyarwa a watan Afrilu na shekarar 2023 kan kudin ruwa na kashi 12.75 cin dari.

Haka ma dai hannayen jarin da suka kai na Naira biliyan 40 ma zai balaga ne bayan shekara 7 watau watan Maris 2025 akan kudin ruwan da suka kai kaso 13.53 cikin dari.

Sauran Naira biliyan 20 din ita ma haka zalika za'a siyar da hannanen jarin har na tsawon shekaru 10 watau zuwa watan fabreru na shekarar 2028 akan kudin ruwa na kaso 13.98 cikin dari.

A wani labarin kuma, sanatocin Najeriya a majalisar dattawan kasar a ranar Talata tayi jimamin mutuwar wasu 'yan Najeriya a hatsarin jirgin saman Itofiya da ya rutsa da su mai lamba ET 302 a satin da yagabata ciki hadda wani fitaccen Farfesa.

Farfesa Pius Adesanmi na adabi a wata jami'ar kasar Kanada kuma dan asalin kasar Najeriya da Mista Abiodun Bashuwa na cikin manyan 'yan Najeriya da hatsarin ya rutsa da su cikin jirgin mai kirar Boeing 737.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel