Shugaban hukumar jin dadin alhazan jihar Kebbi ya mutu

Shugaban hukumar jin dadin alhazan jihar Kebbi ya mutu

Gwamnatin jihar Kebbi ta sanar da mutuwar Alhaji Bala Sakaba, shugaban hukumar jin dadin alhazai, wanda Allah ya yiwa rasuwa a Abuja a jiya, Talata, 19 ga watan Maris, 2019 bayan ya sha fama da jinya.

Marigayin ya mutu ya bar mata biyu da yara da dama. Tuni aka yi jana'izar sa a garin Zuru da ke jihar Kebbi.

A sakon da gwamnatin ta Kebbi ta fitar a shafinta na Tuwita ta mika sakon ta'aziyya ga iyakin mamacin tare da yi ma sa fatan samun rahamar ubangiji.

Shugaban hukumar jin dadin alhazan jihar Kebbi ya mutu
Shugaban hukumar jin dadin alhazan jihar Kebbi ya mutu
Asali: Twitter

Shugaban hukumar jin dadin alhazan jihar Kebbi ya mutu
Jana'izar shugaban hukumar jin dadin alhazan jihar Kebbi
Asali: Twitter

Shugaban hukumar jin dadin alhazan jihar Kebbi ya mutu
Marigayi Alhaji Bala Sakaba
Asali: Twitter

A wani labari na Legit.ng kun ji cewar Shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, ya bayyana cewar nasarar da jam'iyyar APC ke tutiyar ta samu a zabukan da aka kamma ba mai dore wa ba ce.

Shugaban majalisar ya bayyana haka ne jim kadan bayan kammala taron kwamitin zartar wa (NEC) na gaggawa da jam'iyyar PDP ta kira a yau, Laraba, a Abuja.

DUBA WANNAN: Maimaita zabe: Rundunar sojin sama ta fara jigilar kayan aiki zuwa jihohi

Saraki ya bayyana cewar sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabrairu asara ce ga kasa baki daya ba iya kawai jam'iyyar PDP ba.

A ranar 27 ga watan Fabrairu ne hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana shugaba Buhari na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar shugaban kasa.

A sanarwar INEC ta bakin shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shugaba Buhari na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 15,191,847 yayin da babban abokin hamayyar sa, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 11,262,978.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel