Duk karya ce: Har yanzu ina cikin jam'iyyar PDP - Dan takarar gwamnan Legas

Duk karya ce: Har yanzu ina cikin jam'iyyar PDP - Dan takarar gwamnan Legas

Dan takarar gwamnan jihar Legas karkashin jam'iyyar PDP a zaben gwamnan da aka gudanar a ranar 19 ga watan Maris, 2019, Jimi Agbaje ya bukaci al'umma da su yi watsi da wata jita-jita da ake yadawa na cewar ya fice daga jam'iyyar PDP.

A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawunsa, Modupe Ogunbayo, ta ce Agbaje na cikin jam'iyyar daram-dam.

A cewarta: "A awanni 24 da suka gabata, Mr Olujimi Agbaje, dan takarar gwamnan jihar Legas karkashin jam'iyyar PDP a zaben gwamnan da ya gabata, ya karbi kiran wayoyi da sakonni da dama daga abokansa, abokan takararsa a siyasa da ma magoya bayansa, na cewar ya yi murabus daga PDP.

KARANTA WANNAN: Jihar Bauchi: PDP ta lashe zaben kujerar dan majalisar dokokin Tafawa Balewa

Duk karya ce: Har yanzu ina cikin jam'iyyar PDP - Dan takarar gwamnan Legas
Duk karya ce: Har yanzu ina cikin jam'iyyar PDP - Dan takarar gwamnan Legas
Asali: Depositphotos

"Har yanzu Agbaje mamban jam'iyyar PDP ne. Kuma zai ci gaba da kasancewa mai biyayya ga shuwagabanni da ita kanta jam'iyyar, wanda kowa ya san cewa shi ne zai ci gaba da kasancewa abun sha'awa ga al'ummar Legas da Nigeria baki daya.

"Wannan kawai jita jita ce da ake yadawa domin cimma wata mummunan manufa ta siyasa akan Agbaje, da wannan kuma ya ke bukatar daukacin al'umma da su yi watsi da wannan jita jitar, domin ba ta gindi bare tushe," a cewar sanarwar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel