Jam’iyyar PDP ta kalubalanci sakamakon zabe n jihar Nasarawa a kotu

Jam’iyyar PDP ta kalubalanci sakamakon zabe n jihar Nasarawa a kotu

- Jam'iyyar PDP reshen jihar Nasarawa ta bayyana cewa ta shigar da kara kotun zabe

- PDP dai na neman a sake sabon zubi kan sakamakon zaben gwamna, da majalisun dokokin kasa da jiha a jihar

- Jam'iyyar ta sha alwashin kwato kuri'unta da tace an yi mata magudin su

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Nasarawa ta bayyana cewa ta shigar da kara kotun zabe inda ta nemi a sake sabon zubi kan sakamakon zaben gwamna, da majalisun dokokin kasa da jiha a jihar.

Mista Taimako Sunday-Anyuagbuga, babban sakataren labaran jam’iyyar a jihar a bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar Lafia a ranar Laraba, 20 ga watan Maris.

Jam’iyyar PDP ta kalubalanci sakamakon zabe n jihar Nasarawa a kotu
Jam’iyyar PDP ta kalubalanci sakamakon zabe n jihar Nasarawa a kotu
Asali: UGC

A cewarsa, tuni jam’iyyar ta fara bin tsarin kundin tsarin mulki wajen neman hakkinta game da zaben ta hanyar shari’a.

“Jam’iyyar PDP na buri sanar da magoya bayanmu da masu fatan ci gabanjihar Nasarawa cewa mun fara bn tsarin dawo da kuri’unmu da aka sace a kotu.

“Mun shigar da karanmu akan zaben majalisun dokoki da jiha gaban kotu zabe da ke Lafia,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta dage sauraron karar zaben gwamnan jihar Bauchi

A wani lamari na daban, mun ji cewa jam'iyyar PDP ta kira wani taron kwamitin zartar wa (NEC) a gaggauce domin tattauna batun maimaita zaben gwamna da za a yi a wasu jihohi 6 ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

Majiyar Legit.ng da ke da masaniya a kan taron ta shaida ma na cewar jam'iyyar za ta yi amfani da wannan damar domin tattauna wa a kan karar kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da Atiku ya shigar a gaban kotu. Tun kafin zaben shugaban kasa jam'iyyar PDP ke nuna shakku a kan yiwuwar samun adalci a zabukan da za a yi cikin shekarar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel