Yadda APC tayi amfani da sojoji wajen tafka magudi - Buba Galadima

Yadda APC tayi amfani da sojoji wajen tafka magudi - Buba Galadima

Buba Galadima, kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, ya zargin jam'iyyar APC mai mulki da yin amfani da dakarun soji wajen razana ma su zabe domin samun damar tafka magudi a zaben da aka kammala.

Da ya ke magana a wani shirin gidan talabijin na 'Channels' mai taken 'Sunrise', Galadima ya ce abinda ya faru a jihar Ribas yayin zaben gwamna ya isa zama hujja.

"Ba zargi ba ne, kamata yayi ma kotun tuhumar manyan laifuka ta fara tuhumar rundunar sojojin Najeriya.

"Da idona na gani a talabijin yadda sojoji ke bi gida-gida suna kashe mutane," a cewar Galadima.

Jam'iyyar APC a jihar Ribas ta ce hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) a Ribas ta hada baki da gwamnan jihar, Nyesom Wike, tare da sanar da sakamakon na gan-gan a zabukan jihar.

A yayin da APC ke yaba wa dakarun soji bisa kokarin su na tabbatar da tsaro yayin zabe, jam'iyyar PDP Alla-wadai ta yi da rawar da dakarun sojojin su ka taka yayin zaben. A ranar Litinin ne rundunar soji ta musanta zargin da PDP ke yi ma ta.

Yadda APC ta yi amfani da sojoji wajen tafka magudi - Buba Galadima
Buba Galadima
Asali: UGC

Galadima ya bayyana cewar akwai isassun shaidu da su ka tabbatar da cewar dan takarar PDP, Aiku, ne ya lashe zaben shugaban kasa.

"Sun ce su ne su ka yi nasara a zabe amma kuma su na son zuwa kotu domin sake duba kayan aikin zabe, hakan ya nuna cewar sun tafka magudi a zaben.

DUBA WANNAN: Da dumin sa: PDP ta kira taron kwamitin zartar wa cikin gagga wa

"Ina da tabbasa a kan maganganun da nake fada kuma zan iya kare na kai na a gaban kotu.

"Ka taba jin in da wanda ake kara a kan nasarar da ya samu a zabe ya nufi kotu domin neman a bashi damar ya duba takardun sakamakon zabe saboda 'wai' bashi da tabbcin cewar wakilan sa sun yi abinda ya dace?," a cewar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel