Buhari ya yi watsi da wasu kudiri 5 da majalisa ta amince da su

Buhari ya yi watsi da wasu kudiri 5 da majalisa ta amince da su

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake watsi da wasu kudurori biyar da Majalisar Tarayya da aike masa domin neman amincewarsa.

Kudurorin sun hada da na kafa Cibiyar Fina-finai na Najeriya mai taken Nigerian Film Commission bill, sai kuma na yiwa Hukumar Immigration garambawul wato Immigration Amendment bill 2018.

Buhari ya yi watsi da wasu kudiri 5 da majalisa ta amince da su
Buhari ya yi watsi da wasu kudiri 5 da majalisa ta amince da su
Asali: Twitter

Sauran sun hada da kudirin kafa cibiyar kula da canjin yanayi wato Climate change bill 2018, sai kuma na kafa wata cibiya da za ta rika kulawa da kwararun ma'aikatan fansho mai suna Chartered Institute of Pension Practitioners bill 2018 da kuma Digital Rights and Freedom bill.

DUBA WANNAN: 'Yan Majalisun Arewa ta tsakiya sun bukaci a basu kurejar Kakakin Majalisa

Shugban kasar ya sanar da matakin sa na kin amincewa da kudurorin ne cikin wata wasika da aka karanta a zauren majalisar a ranar Laraba.

Dalilan da shugban kasar ya bayar na rashin amincewa da kudirorin kamar yadda ya ke cikin wasikar sun hada da maimaicin ayyuka da wasu hukumomin gwamnati ke yi, tabarbarewar al'amurra da wasu kudurorin za su iya haifarwa da kuma rashin gamsassun bayani a kan wasu kudurorin.

Wannan na zuwa ne kwanda daya bayan Shugaban kasar ya yi watsi da wasu kudirori biyu da majalisar ta aike masa. A halin yanzu adadin kudirorin da shugba Muhammadu Buhari ya yi watsi da su a 2019 sun kai 13.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel