Jami’ar Bayero ta Kano ta samu karin Malamai gangaran guda 36

Jami’ar Bayero ta Kano ta samu karin Malamai gangaran guda 36

Majalisar gudanarwa ta jami’ar Bayero dake Kano, BUK, ta amince da kara ma wasu manyan Malamanta girma zuwa mukamin Farfesa, ko kuma ace gangaran kafi gwani, wani gwani ciki fal shakku, da kuma wasu malamai 40 da suka kai matsayin mataimakin Farfesa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jami’a mai kula da bayanan dalibai dana Malamai, Fatim Mohammed ce ta sanar da haka a ranar Talata, 19 ga watan Maris, inda tace majalisar gudanarwar jami’ar ta dauki wannan mataki ne a yayin zamanta karo na 6 da tayi a ranar Alhamis data gabata.

KU KARANTA: Rayuwata na cikin hadari don Allah ku taimakeni – Inji Alaramma Ahmad Sulaiman

Jami’ar Bayero ta Kano ta samu karin Malamai gangaran guda 36
Jami’ar Bayero ta Kano
Asali: UGC

“Majalisar gudanarwa ta BUK ta amince da karin girma ga wasu manyan Malamai 36 zuwa mukamin Farfesa, da malamai 40 zuwa mukamin mataimakan Farfesa, sai kuma wasu jami’an jami’ar guda 8 zuwa mukamin mataimakan Rajistra, mataimakan Basa da mataimamin Darakta.” Inji sanarwar.

Wasu daga cikin wadanda suka samu karin girman sun hada da Dakta Basheer Abdulkadir Zubair Chedi Farfesa a ilimin magungun, Dakta Musa Aliyu Frafesan magungun, shugaban kungiyar ASUU reshen BUK, Dakta Magaji Barde, Farfesan ilimin kididdiga.

Sauran sun hada da Farfesa Kabiru Tahir Hamid na tsangayar kudi da kididdiga, Ahmad Magaji na sashin harsunan Najeriya, Ya’u Haruna Usman Farfesan yaki da jahilci, Farfesa Abubakar Jika Jiddere na sashin ilimin alakar kasa da kasa, Muhammad Haruna Awaisu, Emmanuel S Kolo da Lofty-John Chukwuemeka.

Haka nan akwai mata uku daga cikinsu da suka hada da Dije Muhammad Sulaiman da Hannatu Sabo daga tsangayar kudi da kididdiga, da kuma Amina Mustapha daga tsangayar ilimin noma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel