Da dumin sa: PDP ta kira taron kwamitin zartar wa cikin gagga wa

Da dumin sa: PDP ta kira taron kwamitin zartar wa cikin gagga wa

Jam'iyyar PDP ta kira wani taron kwamitin zartar wa (NEC) a gaggauce domin tattauna batun maimaita zaben gwamna da za a yi a wasu jihohi 6 ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

Majiyar Legit.ng da ke da masaniya a kan taron ta shaida ma na cewar jam'iyyar za ta yi amfani da wannan damar domin tattauna wa a kan karar kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da Atiku ya shigar a gaban kotu.

Tun kafin zaben shugaban kasa jam'iyyar PDP ke nuna shakku a kan yiwuwar samun adalci a zabukan da za a yi cikin shekarar nan.

Da dumin sa: PDP ta kira taron kwamitin zartar wa cikin gagga wa
PDP ta kira taron kwamitin zartar wa cikin gagga wa
Asali: Facebook

PDP ta sha bayyana cewar jam'iyyar APC mai mulki na shirin tafka magudi a zaben shugaban kasa da ragowar zabukan da za a yi.

DUBA WANNAN: Zaben 2019 a Najeriya mummunan labari ne ga dimokradiyya – Amurka

Tun kafin a kai ga sanar da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar 23 ga watan Fabrairu, 2019, jam'iyyar PDP ta bukaci hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) ta dakatar da tattara sakamakon zabe daga jihohi bisa zargin cewar an tafka magudi a zaben.

Jim kadan bayan INEC ta sanar da shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi watsi da sakamakon zabe da bayyana cewar zai kalubalanci sakamakon zaben a kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel